Maigadin katafaren ginin shaguna na Banex dakr Abuja, Clement Sargwak, ya bayyana wa PREMIUM TIMES, cewa shufaban hukumar CCT Danladi Umar ya yi masa dukan rashin Imani kawai don ya roke shi ya gyara motarsa da ya ajiyae ba daidai ba.
Sargwak ya ce karamin duka ya sha ba.
” Motar Danladi Umar ya shigo cikin harabar kasuwar, sai yayi fakin ba daidai ba. A matsayi na na maigadi kuma mai kula da yadda ake ajiyar motoci sai na je na same sa, na ce masa Yallabai ka dan gyara motar ka saboda ka kare masu fita.
” Bude motar sa ke da wuya sai ya gaura min mari, na dan ja da baya kadan a lokacin ya fito daga cikin motar sa. Ya na sauka daga motar sai ya rika daddalla min mari yana tokari na. Da na mike tsaye sai ya tokare ni ya sharamin mari.
” Wannan duka bai tsaya daga shi Ogan ba, idan ya shararamin mari ya tokari, sai ya ce wa direban sa shima ya gaura min mari, haka shima sai ya ware hannu ya dalla min mari ta hagu, idan na juya ta dama kuma sai shugaban CCT Danladi Umar ya tokare ni. Abin fa ya kai ga har sai da ya Umar dan sandan dake motar sa ya rika jibga ta shima ta baya.
” Daga nan dai na samu na arce zuwa wajen ogan mu a Filaza din. Wadanda suka zo taimakona ma ba su tsira ba.
Sargwak ya ce daga baya yan sanda sun tafi da shi a umarnin Danladi, a nan suka dauki jawabin sa. Sai dai bayan DPO ya kalli bidiyon abin da ya faru, ya girgiza kai ya ce in yi tafiyata.
Daga baya Lauyan wannan kasuwa ya ce an samu labarun shi Danladi Umar din ya dawo da dare, sannan wasu jami’an tsaro cikin fararen kaya sun dauki jawabin Sarwag sun kuma dauki hotonsa.