An yi wa ’yan sanda uku kisan gilla a ranar Talata, wurin gangamin da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Charles Soludo ya shirya, a jihar Anambra.
Har ila yau kuma a wurin wasu ’yan sandan hudu sun bace babu labarin su har zuwa lokacin rubuta wannan labari.
Wasu ’yan bindiga ne da ba a san ko su wane ba, a ranar Laraba su ka kashe jami’an tsaron su uku, wadanda ke tsaron lafiyar tsohon Gwamnan CBN, Charles Soludo.
Wannan kisa ya kara fitowa fili da barazanar kisan da ake ci gaba da yi wa jami’an tsaro na ’yan sanda, musamman a kudancin kasar nan.
An bindige su ne a Isoufia, garin su Soludo, cikin Karamar Hukumar Aguata, cikin Jihar Anambra sauran jami’an ‘yan sanda hudu sun ji ciwo a lokacin da aka kai masu harin, amma dai shi Soludo ya tsallake rijiya da baya.
Sannan kuma an yi garkuwa da Emeka Ezwnwanne, wanda kwamishina ne a Jihar Anambra. An yi garkuwa da shi ne yayin da aka kama shi a wurin gangamin Soludo.
Wanda mummunan lamarin ya faru a gaban sa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara ne su ka tarwatsa taron gangamin Soludo yayin ganawar sa da matsan kauyen sun a Isoufia.
Ya ce lamarin ya faru a dandalin taron jama’ar kauyen.
“An kashe ’yan sanda uku, an ji wa wasu raunuka. Shi kuma Soludo ya yi sauri ya bar jihar jim kadan bayan faruwar lamarin.
Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sanda a Jihar Anambra, Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Amma kuma ya ce bai san takamaimen yawan jami’an tsaron da aka bindige ba.
Shi kuwa kakakin yada labarai na Soludo, mai suna Pauly Onyeka, ya bayyana cewa tsohon gwamnan na CBN bai ji rauni ba, lafiyar sa garas.
Ganin yadda ake ta samun gagarimar matsalar tsaro a fadin kasar nan har Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, a cikin makonni biyun da su ka gabata ya nuna fargabar cewa matsalar tsaro ka iya hargitsa zaben 2023.
Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, ya gargadi Gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar matakan dakile matsalar tsaro tun da wuri, idan ba haka ba kuwa, to za a iya fuskantar mummunan zubar da jini a zaben 2023.
Akeredolu, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kudu maso Kudu, ya yi wannan tsokaci ne kan tabarbarewar matsalar tsaro a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels, a ranar Talata.
Ya fara da buga misalin harin da aka kai wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai, wanda ya ce wannan kadai ya isa kowa ya gane cewa babu tsaro a kasar nan.
Yayin da ya ke ganawa da Shugaba Buhari a ranar Talata, ya yi gargadin cewa rashin tsaro ka iya hargitsa zaben 2023.
“Wato ni ina ganin cewa gaskiya ne ba za muiya gudanar da zabe a wannan halin yanayi na rashin tsaro ba kasar nan. Don haka idan ba a kawar da matsalar tsaron nan ba, to hare-haren ’yan bindiga zai karu matuka, ta yadda ba zai yiwu a gudanar da zabe ba, ko kuma a rika zubar da jini a lokacin zabe.
“To idan aka yi sake aka kai ga wannan mummunan yanayin da ba fatan kaiwa ake yi ba, wa ke ta wani zancen zabe kowa ta neman tsira da ran sa.”
“Saboda haka wajibin gwamnatin tarayya ne ta kawar da wannan matsalar tsaro domin kowa ya huta a kasar nan.”
Akeredolu kuma ya kara da cewa wannan matsalar tsaro ba za a iya kawar da ita dindindin ba har sai an kyale jihohi sun kafa yan sandan jihohi tukunna.