Babban abin da ya dade yana ci wa yankin Arewa tuwo a kwarya shine yadda za a bunkasa bangaren ilimi a yankin da yadda zai yalwata kuma ya kai ga talaka, wato shima talaka ya iya samun wannan ilimi na zamani.
Kukan mutanen Arewa bai wuce kukan tabarbarewar ilimi da yankin ke fama da shi ba. Gwamnatocin baya har da na yanzu ba su yi wa bangaren ilimi gwaninta a jihohin su. Idan ka garzaya makarantun gwamnati sai hankalinka ya tashi ka rasa inda za aka saka kanka saboda karancin makarantun kwarai da malamai masu nagarta da kishi.
Idan ka duba yadda manyan makarantu suke a kudancin Najeriya zaka tabbatar cewa lallai babu makarantu a yankin Arewacin Kasar. A nan ina maganan manyan makarantu.
A jihar Legas, Ogun, Oyo, Osun da Edo manyan karantu na gaba da sakandare sun kusa yin kan-kan-kan da makarantun firamare a jihohin.
A jiha daya kawai akwai jami’oi da makarantun gaba da sakandare fiye da 10. Sannan kuma basu kai Arewa yawan mutane ba. Banda jihar Legas kusan sauran duka ba su wuce jihohin Kano da Kaduna yawa ba gaba dayan su.
A haka dai abin na damun wasu ‘yan arewa da ke ganin lallai fa dole sai an farfado daga barcin da ake a tunkari warware matsalolin maganar ilimi tukunna kafin a iya samun cigaba mai ma’ana a yankin.
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Farfesa na farko a Arewa da ya kai matsayin farfesa cikin kankanin shekaru. Wannan baiwa ne da Allah yayi masa da kuma karamci ga yankin Arewacin Najeriya domin bayyanar sa ke da wuya sai komai ya canja.
Farfesa Gwarzo ne shugaban jami’ar Maryam Abacha dake Nijar. Wannan jami’a itace ta farko da ke koyar da dalibai da harcen turanci a yankin Kasa rainon Faransa.
Kafa wannan makaranta ke da wuya sai ta fara haskawa, dalibai suka fara tururuwa zuwa jami’ar babu kakkautawa a ko’ina a fadin kasashen Afirka.
Wani abin a yaba da farfesa Gwarzo yayi domin kasar sa Najeriya, shine bada tallafin guraben karatu wa musamman ‘yan Najeriya.
A duk shekara sai an dibi dalibai masu yawa daga Najeriya wanda za a basu tallafi tun daga farkon karatun su har karshe babu ko sisi da za su biya.
Wannan kokari da himma na Farfesa Adamu Gwarzo ya samu yabo da jinjina daga mutanen Najeriya inda ya ke samun addu’oi da sambarka a ko da yaushe.
Hakan bai gamsar da limamin cigaban ilimin ‘yan Arewa ba, Farfesa Gwarzo sai yayi abin ban mamaki kuma.
An wayi gari ne kawai anji ashe tuni ya mika takardar a amince masa ya kafa irin wancan jami’a da ya kafa a Nijar a jihar sa ta haihuwa wato jihar Kano.
Gwamnatin Najeriya kuwa ta yi na’am da wannan bukata tasa ta rattaba hannu akai ta danka masa takardar amincewa, tare da wasu jami’oi da suka nemi haka.
Gogan naka daga nan sai barci ya yanke masa, ta tattara ya maida hankali wajen ganin an kammala jami’ar da ake gina wa a Kano.
Wannan gini na jami’a ya kai gini sannan kuma an samar da duk wani abu da za a bukata a kowacce jami’a a fadin duniya. Malam sai dai ka gani.
Wannan himma tasa bai tsaya nan ba, baya ga kokarin haka da ya maida hankali a kai, sai kuma ya ce a Kano bai ishe shi ba ya garzayo jihar Kaduna itama don kafa jami’a irin haka.
Baya ga na sa da yake kakkafawa domin al’ummar Arewa, wadanda ma mallakin gwamnatin Najeriya ne Farfesa Adamu Gwarzo bai barsu haka, yana bi yan rarraba musu manyan motocin daukan daliba, motocin daukan marasa lafiya da kuma tallafi dabam dabam wanda ke wanzuwa a karkashin gidauniyar sa AAG.
Sannan kuma baiwar da Allah yayi masa ba shi da girman kai da nuna isa ba, kamar yadda wasu ke yi. Kowa na sa ne, duk inda ka nufe shi da abu na arziki zai yi iya kokarinsa yaga ka yi nasara akai.
Idan nace zan cigaba da fadin abubuwan da Farfesa Gwarzo yake shukawa domin ci gaban ilimi a yankin Arewa sai mu kwana muna rubutu.
Amma bari in tsaya hakanan, rokon mu da fatan mu shine Allah ya yawaita wa Arewa irin sa matashi mai kishin Arewa da mutanen yankin gaba daya.