Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana yadda ta ce ta yi wa Boko Haram raga-raga, a wani shigar-kutse da ’yan ta’addar su ka yi wa Damasak, garin da ke kan iyaka a Jihar Barno.
Baya ga fatattakar ‘yan ta’addar da sojojin Najeriya su ka bayyana cewa sun yi, sun kuma sanar cewa sun kashe wasu ’yan Boko Haram din, a darkaken da su ka yi masu a Damasak, hedikwatar Karamar Hukumar Mobbar da ke Jihar Barno.
Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Mohammed Yarima ne ya fitar da wannan bayani a ranar Litinin, cewa sun samu wannan gagarimar nasara a kan Boko Haram a ranar 10 Ga Afrilu.
“Zaratan dakarun mu sun darkaki mayakan Boko Haram, inda su ka rika kai masu hare-hare ta sama da kasa. Wannan ya sa kowa ya tarwatse daga gungun da su ka yi. Da yawan su sun tsere da manyan raunuka, wasu kuwa sun mace nan take.”
Yerima ya kara da cewa Boko Haram sun gudu sun bar wasu motocin su na yaki da makamai da dama.
Sannan kuma ya kara da cewa an rasa sojoji biyu a wurin bata-kashin da aka yi da Boko Haram.
Wannan bayani na Hukumar Sojojin Najeriya, ya zo ne kwana daya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da an kai mata hari a Damasak, inda ta kara da cewa harin da Boko Haram su ka kai wa UN zai rage ayyukan agajin da ta ke yi a Barno.
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa harin da BokoHaram su ka kai wa wasu kayayyakin ta a Damasak da ke jihar Barno, zai takaita ayyukan jinkai da agajin da UN din ke yi a yankin.
Babban Jami’in Kula da Ayyukan Agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon ne ya bayyanar da haka, tare da tabbatar da cewa an kai wa kayan UN hari kuma an lalata su.
Cikin wata sanarwa da Kallon ya aika wa PREMIUMTIMES, ya nuna matukar damuwar UN a kan harin da ake kai wa da ya ce rayukan fararen hula na kara shiga cikin hatsari.
“Ranar Asabar an kai wa sansanin kayan UN da na wasu kungiyoyin agaji masu masu hadin guiwar ayyukan agaji tareda UN su uku, duk aka lalata masu kayayyaki, aka banka masu wuta.
Yayin da ya ke yin tir da harin da kuma nuna damuwa, ya ce wannan aika-aika da aka yi za ta tilasta Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin bada agajin su takaita ayyukan jinkan da su ke gudanarwa a yankin Damasak.
“Wannan hari zai shafi ayyukan jinkai da agajin da mu ke bai wa mutane 8,000 da aka fatattaka daga gidajen su, da kuma wasu mutum 76,000 da ke cikin yankunan karkara daban-daban na yankin wadanda ake agaza wa kuma su ke bukatar tsaron rayukan su a yankin.”
A ranar Lahadi ce PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin Boko Haram sun banka wa kayan UN wuta bayan sun kashe sojoji da farar hula a Damasak, har su ka kashe mutum hudu.
Sai dai kuma wadanda su ka mutu din kamar yadda wani karin bayani ya tabbatar daga baya, sun kai mutum bakwai.
Akalla mutum hudu cikin su har da sojoji ne Boko Haram su ka kashe a wani mummunan hari da su ka kai a Damasak, gari da ke kan iyakar Jihar Barno.
Majiya ta bayyana cewa Boko Haram ‘yan bangaren ISWAP ne su ka kai wannan hari, inda bayan kashe mutumm hudun, sun kuma kai farmaki a kan wasu kayan Majalisar Dinkin Duniya, ofishin ‘yan sanda da kuma wani asibiti.
Wasu bayanai da su ka fito daga garin wanda ke kan iyaka, an tabbatar da cewa ISWAP sun kai harin da a ranar Asabar. Amma dai zuwa yanzu babu wani karin haske game da ko an samu karin asarar rayuka zuwa yau Lahadi da safe.
“Lamarin ya yi muni kwarai da gaske a ranar Asabar, a lokacin da Boko Haram su ka dira Damasak da rana tsaka.” Haka wata majiyar jami’an tsaron sa-kai ta bayyana wa PREMIUM TIMES, kuma ta nemi a sakaya sunan ta.
“Mahara din sun yi jerin gwano ne a kan babura dauke da zabga-zabgan bindigogi wasu kuma na kan motocin yaki.
“Sun kai hari a zansanin ofishin Majalisar Dinkin Duniya, su ka banka masa wuta.
“Sannan kuma sun yi wa wasu mutum biyu yankan rago. Daga baya kuma mu ka gano cewa sun kashe wasu zaratan sojoji biyu.”
“Tabbas kuma sun banka wuta kan wani wuri na Majalisar Dinkin Duniya da GISCOR da INTERSOS da NRC duk da haka kuma su ka saci motoci yayin kai wa sauran wuraren hare-hare.
“Boko Haram sun kuma zarce har Babban Asibitin Damasak su ka yi awon gaba da magunguna da kayan da su ka danganci amfanin majiyyata. Amma a wurin wani Kwamandan su ya hana su banka wa asibitin wuta, saboda akwai marasa lafiya kwance a asibitin.”
PREMIUM TIMES ta gano cewa har ofishin ‘yan sanda na Damasak Boko Haram sai da su ka kai wa hari a ranar.
“Harin da aka banka wa kayan Majalisar Dinkin duniya wuta, ya shafi wasu runbunan ajiyar kayan agaji na wasu kungiyoyi, ciki har da ACTED, duk sun ci wuta.
Majiya ta ce maharan sun arce da motar daukar maras lafiya ta asibitin Damasak da kuma wasu motocin daban.
‘Fashewar Bam a Tsakiyar Mutane’
Wasu ‘yan garin Damasak sun yi ikirarin cewa wani jirgin yaki ya kai dauki, amma an samu kuskure ya jefa bam cikin gungun masu taro radin suna a cikin wani gida, har ya kashe mutane da yawa manya da kananan yara.
Amma dai PREMIUM TIMES ta kasa tantance gaskiyar wannan lamari na jefa bam.
Discussion about this post