Wadannan matasan da aka gani a wani bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo a jibar Kogi ana zane su da bulala na tsare a ofishin’ Yan sanda.
Idan ba a manta ba wasu matasa su biyu sun shiga hannun matasan Kogi a daidai suna zanga-zangar kira ga Bubari ya yi murabus rike da fastoci sannan kuma sun rubuta a bango cewa ‘ Buhari ya ajiye mulki’.
Sai dai hakan su bai cimma ruwa ba domin wasu matasa sun take su a wannan wuri inda suka tilastasu su goge wannan rubutu sannan kuma suka tsatsaula musu dorina a dia dai suna govewa.
Bayan haka suka tilasta su su cinye wannan fastoci da suke rike dasu.
An rika jin matasan na cewa sai sun fadi wanda ya aiko su jibar kogi su zo su yi zanga-zangar kiyayya ga Buhari.
” Mu a jihar Kogi Buhari mu ke yi 100 bisa 100, ba mu gayyaci wani ya zo yayi mana kamfen din kiyayya ga Buhari ba. Kawai ku tsallako tun daga jihohin ku ku zo mana jiha wai kuna kamfen din kiyayya ga shugaba Buhari, ba ku isa ba.” In ji Matasan Kogi.
Bayan haka jami’an yan sanda sun yi awon gaba da su.
Yanzu dai suna tsare ana gudanar da bincike akai.