Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana wa mutanen Kaduna cewa duk abin da gwamnatin sa ke yi, ta na yi don jama’ar jihar ne da ci gaban su.
A hira da yayi da manema labarai a fadar gwamnati dake Kaduna, El-Rufai ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa gwamnati ke tsananta karbar haraji da kuma sallamar ma’aikata da ake yi a kananan hukumomin jihar.
Sannan kuma ya kara da cewa Korona ta fallasa ma’aikatan jihar dake cin bulus ba su aiki sai dai su jira albashi kawai.
“Abinda ya sa mutane ke yin abinda suka dama game da Korona shine saboda gwamnati na yi musu abinda suke so, daga karshen wannan wata kowa ya kamu zai biya kudin magani da kudinsa”
“Mun samu kudin gina titin dogo a Kaduna, zamu gina daga Maraban Jos zuwa NNPC kuma zai dauke mu shekaru biyu, da wannan tsari za mu fara”
” Duk wanda bashi da takardar mallakan gida na kantoma na tun zamanin da, da takardar izinin gini, ba za mu biya shi ko sisi ba idan gwamnati ta zo aiki wannan unguwa. Kowa ya je ya sabunta takardunsa, ya kuma biya harajin gidan.
” Ko da’ na aka kama ba zan biya ko sisi ba sai dai in je in yi ta addu’a Allah ya saka ka a Aljannah, don ba zan biya ko sisi ba. Saboda haka su yi taka-tsantsan ”
” Hatta wadanda ke aiki tare da mu wato wadanda muka nada, suma za su rage su, muna nan muna dubawa. Za muce cin ‘banzan ya isa’ za mu ce abin ya isa haka aje ayi wani abin”
” Korona ta tona asirin wasu ma’aikata da yawa a jihar Kaduna, mun gano ashe ba sai an yi da wasu da yawa ba a aikin gwamnati. Daga na sama da kananan ma’aikata, na tsakiya ba su komai ”
” Korona ta tona asirin wasu ma’aikata da yawa a jihar Kaduna, mun gano ashe ba sai an yi da wasu da yawa ba a aikin gwamnati. Daga na sama da kananan ma’aikata, na tsakiya ba su aikin komai ”
Discussion about this post