Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa a shirye yake ya baiwa fannin shari’a cin gashin kanta a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka lokacin da yake rantsar da sabon babban jojin jihar na kotunan shari’ a, Mohammed Abubakar.
” Ba tun yanzu ba na yi na’am da wannan batu na baiwa fannin sharia cin gashin kai. Na yarda da wannan tsari domin hakan zai baiwa fannin damar yin aiki yadda yakamata kamar yadda doka ya ke a dokar kasa.
” Da fannin shari’a ne talaka ya dogara, ba talaka ba hatta ni kai na Bala na amfana da fannin. Saboda haka a shirye nake mu baiwa fannin cin gashin kanta kai tsaye.
A karshe ya hori saban babban Alkali Abubakar, ya maida hankali waken yin aiki tukuru domin ci gaban fannin shari’ar jihar da jihar baki daya.
Discussion about this post