Jami’an Sibul Difens sun damke wani matashi da da ya kashe wata mata wajen yi mata fyade

0

Jami’an tsaro na Sibul Difens a jihar Kwara sun damke wani matashi mai shekaru 19 mai suna Sadiq Adams da ya kashe wata mai Aishat Sanni a daidai yana yi mata fyade.

Kakakin hukumar Babawale Afolabi ya sanar da haka wa manema labarai a jihar.

Afokabi ya ce jami’an tsaron sun kama abokan Adams guda uku da suka hada da Rasaq Rasheed, mai shekaru 16; Lukman Quadri, mai shekaru 15; da Billiaminu Qayum, mai shekaru 16.

Ya ce Adams ya danne Aishat a wani gonar kashu dake kauyen Esie a karamar hukumar Irepodun ranar Juma’an da ya gabata.

“Adams da abokanan sa sun kama Aishat da wata matan Bororo bayan sun kama su da laifin satan kwallon kashu. “Adams ya tsare Aishat sannan ya aiki abokansa su kamo dayar matar dake satan kwallo kashu tare da Aishat da ta gudu amma ba su kamo ta ba.

” Kafin su dawo Adams ya danne Aishat da karfin tsiya, garin haka ta yi sallama da duniyan.

Afolabi ya ce Aishat ta ciji Adams a hannu sannan ta kwajiresa a wuya yayin Adams ke kokuwa da ita.

Ya ce Adams da abokansa uku na tsare a hannun rundunar ‘yan sandan jihar sannan hukumar gurfanar da masu aikata laifuka irin haka za su ci gaba da bincike akai.

Za a kai su kotu da zaran sun kammala bincike.

Share.

game da Author