Gwamnonin Kudu maso Gabas sun haramta kiwo sakaka a jihohin su

0

Gwamnonin Jihohin yankin Kudu maso Gabas sun haramta kiwo sakaka a jihohin su, sannan kuma sun kafa Jami’an Tsaron Samar da Tsaro na Hadin Guiwa.

A wani taron da gwamnonin su ka shirya a Owerri, babban birninjihar Imo a ranar Lahadi, sun bayyana suna sabuwar Rundunar Hukumar Tsaron Hadin Guiwa da suka samar da suna Ebube Agu, wato ‘Damisa Ki Sabo’.

Gwamna David Omahi na Jihar Ebonyi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnaonin Jihohin kabilar Igbo ne ya yi wa manema labarai bayanin abinda taron ya kunsa.

Ya bayyana cewa an haramta yawo sakaka da dabbobi ana kiwo a jhohin yankin da su ka kunshi Imo, Anambra, Abia, Ebonyi da Enugu

Ya ce sun kafa sabouwar rundunar tsaron ta hadin guiwa ce damin karfafa tsaro a yankin.

Sannan kuma an kafa kwamitin da zai kula da ayyukan da kuma tabbatar da fara aikin jami’an tsaron na ‘Damisa Ki Sabo’.

A wurin taron, gwamnonin sun yi tir da wasu hare-hare da aka kai wa wasu hukumomin tsaro a yankin da su ka hada da Hedikwatar ‘Yan Sanda a Jihar Imo da Gidan Kurkukun Owerri na jihar Imo da sauran wasu ofisoshin ‘yan sanda.

A taron sun yi kira da a samu wanzuwar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyayi da manomi.

Sun kuma nuna goyon baya kan irin kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen dakile matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Share.

game da Author