• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    HANYAR DAMATURU ZUWA BIU: Yadda matafiya ke cin kwakwa Tsawon shekaru 9 an kasa kammala gyaran titin kilomita 125

    Kotu ta kwato maka-makan gidaje 48 a hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF

    KARKATAR DA NAIRA MILIYAN 289: EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Katsina a kotu

    Gwamna Uba Sani ne ya yi  Ruwa ya yi Tsaki a takara ta ba mahaifina El-Rufai ba – Bello El-Rufai

    FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air

    Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto

    Atiku ya kafa gaggan lauyoyi 18, ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu

    SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Atiku ya zargi INEC ta ƙin ba shi kwafen bayanan zaɓe duk da ya biya haƙƙin Naira miliyan 6 kuɗin karɓar bayanan

    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Ku Gina Soyayyar Ku Akan Sarki Sanusi Don Allah, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
April 12, 2021
in Ra'ayi
0
Sanusi Lamido

Sanusi Lamido

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku bayin Allah! Abun da nike son al’ummah su fahimta shine, ita soyayya Allah Sunhanahu wa Ta’ala ne yake dasa ta a cikin zuciyar bayinsa ba tare da ma su sun sani ba. Kawai sai dai kaji kana kaunar mutum, amma baka san yaya aka yi soyayyar ta kullu ba.

Kawai dai abun da ake bukata a wurin ko wane mutum shine, yayi kokarin ganin cewa duk wanda yake so, yana son sa ne ba domin komai ba, sai don Allah. Kar ka yarda ka gina soyayyar ka akan ko wane mutum akan abun duniya mai karewa, ko akan kabilanci, ko wani abu mai kama da haka. Domin da zarar abun ya kare, ko kuma ya gushe, to sai kaji baka son mutum, tun da dama can tun farko, abunda ka gina son sa akai, yanzu babu shi.

Ya ‘yan uwa, a yau zaka tarar, wani yana son wani ne saboda su ‘yan kungiya daya ne, wasu kuma saboda sun hada darika guda, wani kuma saboda yaren su guda, wani saboda garin su guda, wani saboda kasar su guda, wani kuma saboda kusanci na jini… haka dai zaka tarar da mutane daban-daban, kuma masu manufa daban-daban da suka gina soyayyar su akai.

Abun da wasu mutane basu gane ba, kuma basu fahimta ba, game da soyayya ta da Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II shine, soyayyar da ke tsakanin mu an gina tane saboda Allah, kuma tsakani da Allah.

Sarki Muhammadu Sanusi II masoyi nane, kuma amini na ne, na gaske, ba da wasa ba, kuma suruki nane. Allah ne ya hada wannan soyayya tsakanin mu.

A wannan soyayya tamu, babu maganar garin mu daya, ko jihar mu daya, ko mun fito cikin zuri’a daya ne, ko kungiya daya, ko darika daya, da sauran su.

Da farko-farko, nasha suka da zagi da gori da cin mutunci iri-iri daga wurin wasu mutane, akan soyayya ta da Sarki Muhammadu Sanusi II, kafin yanzu daga baya su gane, har su zo suna bani hakuri, kuma ma mu zama abokan juna. Wasu zaka ji sun ce, ina ruwanka da maganar masarautar Kano, tun da kai ba dan jihar Kano bane. Wasu kuma suce ina ruwan ka da Mai Martaba Sarki, tun da kai ba dan darikar tijjaniyyah bane. Wasu kuma da suka hada dangi da Sarkin, zaka ji suna cewa ina ruwan ka da sha’anin abun da ya shafi zuri’ar gidan Malam Ibrahim Dabo. Wasu kuma zaka ji sunce, su suna kin Sarki Sanusi ne, kuma basu son shi, saboda shi dan darikar tijjaniyyah ne, da sauran dai maganganu na cin mutunci da zagi da batanci kala-kala. Amma duk wadannan maganganu ni wallahi sam, basu taba damu na ba. Kuma yanzu alhamdulillahi, da yake mun yi hakuri, kuma ya kasance domin Allah muke yi, duk wadannan abubuwa sun wuce, kuma sun kau, kuma masu yin wannan ma duk sun nemi afuwa, kuma na yafe masu har ga Allah. Yanzu kuma abu guda ya hada mu, shine soyayyar Sarki da kuma kare mutuncinsa.

Ya ku jama’ah, ku sani! Ita soyayya domin Allah abu ne wanda yake da asali sosai a cikin addinin Musulunci, kai addini ne ma kaso mutum saboda Allah. Kuma yana daga cikin ayyukan da suke janyo wa bawa samun kusancin Allah da kuma yardar sa, wadda ita ce kololuwar abun nema a wurin dukkan mumini.

Sannan Idan an duba ta fuskar tarihi ma za’a iya cewa da shine ma addinin nan namu na Musulunci ya ginu. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Halaye guda uku, duk wanda ya kasance yana da su, to ya dace da samun dandanon zakin imani: 1. Ya kasance Allah da Manzon sa sun fi soyuwa a gare shi fiye da wanin su. 2. Ya kasance yana son wani mutum, ba domin komai ba sai domin Allah. 3. Ya kasance yana kin kafirci, bayan Allah ya tsame shi daga ciki, kamar yadda yake kin a jefa shi a cikin wuta.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]

Sannan masu son juna domin Allah suna daga cikin nau’in mutane guda bakwai wadanda Allah (SWT) zai shigar da su a cikin inuwar sa, ranar da babu wata inuwa sai inuwar Allah, a ranar da kusan dukkan halittu suke cikin rudani da wahala da tashin hankali. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Mutum bakwai, Allah zai sa su cikin inuwar sa, a ranar da babu wata inuwa sai inuwar Allah: 1. Shugaba mai adalci 2. Matashi wanda ya rayu a cikin bautar Allah. 3. Mutumin da a koda yaushe zuciyarsa tana rataye da guraren Ibadah (Masallatai). 4. Mutum biyu da suka so juna domin Allah. Sun hadu akan haka, kuma sun rabu akan haka. 5. Da Mutumin da wata mace ma’abociyar kyau da kwalliya, ta kirashi (zuwa fasikanci) sai yace, a’a, ni ina jin tsoron Allah. 6. Da mutumin da zai yi sadaka sai yayi ta a boye, har hannunsa na hagu ya zamanto bai san abin da daman sa yake bayarwa ba. 7. Da mutumin da ya tuna Allah a kebe (shi kadai) har idon sa ya zubar da hawaye.” [Bukhari da Muslim]

Soyayya domin Allah tana san ya wa mutum ya samu wani matsayi na musamman a wurin Ubangijinsa. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Allah (SWT) zai fada a ranar Alkiyamah, yace: “Ina masu soyayya domin girma na, a yau din nan zan zasu a cikin inuwata.” [Muslim]

Kuma Manzon Allah (SAW) yace:

“Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa: ‘Soyayyata ta wajaba ga wadanda suke soyayyar juna domi na, da masu zama da juna domi na, da masu ziyartar juna domi na, da kuma masu ciyar da dukiya domi na.” [Imamu Malik ya ruwaito shi a cikin Muwadda]

Yanzu jama’ah tambayar da zamu yiwa kan mu a nan ita ce, shin wadanne mutane ne a wannan zamanin suka siffantu da wannan baiwar da wannan halayyar ta soyayyar juna ba don neman duniya ko abin cikinta ba… sai dai domin Allah kadai? Lallai wadannan halaye ba in da zaka same su sai a wurin Musulmi nagari, masoyin Allah da Manzon sa (SAW) na hakika, masoyin iyalan gidansa da Sahabbansa baki daya. Duk wani gungun Musulmi masu wannan siffar da ka ziyarta, za ka tarar ma’abotansa mutane ne masu karamci masu mutunci. Zaka tarar duniyar nan bata dame su ba ballantana ta dauki hankalinsu. Kawai suna son juna ne saboda Allah. Kuma zaka tarar a zamantakewar su, babu cuta babu cutarwa, babu yaudara, babu ha’inci ko raini, ko wulakanta juna a tsakaninsu. Abunda zaka tarar tsakanin su shine, girmama juna da hidimtawa kowa. Kuma har kullum, zaka tarar zuciyarsu a wartsake take, domin tana ta’allake da soyayyar Allah, da soyayyar Manzon Allah (SAW), da soyayyar junan su. Basu kin kowa sai wanda Allah da Manzon sa suka ki.

Imam Ash-Shaukani Allah yayi masa rahama yana cewa:

“Wata rana na kwana ina ta kai komo akan Hadisin nan na Manzon Allah (SAW), da yake cewa: “Lallai masu soyayya domin Allah suna kan wani minbari na haske, wanda Annabawa da Shahidai zasu so ace su ne a wannan matsayin”, na kasance ina ta tunani akan wannan Hadisin, ina cewa ta yaya soyayya domin Allah za ta kasance, yaya take ne da za’a ce har Annabawa da Shahidai suna kwadayin samunta? Sai nace; hakika da yawa soyayyar da ake samu a yanzu, wallahi mafi yawanci, ba don Allah ake yin ta ba: An wayi gari, miji zai so matarsa ba domin Allah ba. Mata zata so mijin ta ba don Allah ba. ‘Ya’ya suna son iyayen su ba don Allah ba. Iyaye suna son ‘ya’ yan su ba domin Allah ba. Hakanan zaka ga wasu mutane suna son wani shugaba, ko wani malami, ko wani dan siyasa, ko wani dan kasuwa, ko wani mai wakiltar ka, ba domin Allah ba. Ko kana son wane saboda kyaun sa, ko saboda sautin sa, ko saboda kudin sa. Da wannan ne na gane cewa lallai ita soyayya domin Allah tafi karanci a cikin al’ummah a yau sama da kan kibreet.” [Duba Fathur-Rabbani, mujalladi na 9]

Kuma wallahi ni, babban abun da ya kara sa in kaunaci Sarki Muhammadu Sanusi II tsakani da Allah shine, saboda gaskiyarsa, da amanarsa, da kuma son talakawa, da kaunar ci gaba da yake da ita, sannan kuma da cikakken yakinin da nike da shi na cewa zaluntarsa aka yi. Kuma Allah ma da kan sa, ya umurce mu da mu kasance tare da masu gaskiya a koda yaushe. Allah yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani, kuji tsoron Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya.”

“Wani mutum yazo wurin Manzon Allah (SAW) yace masa, ya Manzon Allah, ina so in kasance tare da kai a cikin Aljannah. Sai Annbai yace masa, to me kayi tanadi domin samuwar hakan? Sai mutumin yace, ban tanadi komai ba illa son ka ya Rasulullah. Sai Annabi (SAW) yace: Lallai ko wane mutum yana tare da wanda yake so.”

Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi II, bamu ma fara son sa da kaunar sa ba da ikon Allah!

Daga karshe, ina rokon Allah ya kara muna soyayyar Allah da Manzon sa (SAW), da kuma soyayyar junan mu tsakani da Allah, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Tags: AbujaHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMESSarki Sanusi
Previous Post

EL-CLASSICO: Messi ya jera wasanni 7, tun tafiyar Ronaldo bai kara jefa kwallo a ragar Real Madrid ba

Next Post

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun haramta kiwo sakaka a jihohin su

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Gwamnan Ebonyi, David Umahi ya kamu da Korona

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun haramta kiwo sakaka a jihohin su

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • TATTALIN ARZIKI: Ɗanyen man Najeriya ya fara kwantai a duniya, bayan Chana, Turai da Indiya sun koma sayen na Rasha mai rahusa sosai
  • HAJJI 2023: Hukumar Alhazai ta gindiya sabbin sharuɗɗan adadin kwanakin ziyara Madina
  • HANYAR DAMATURU ZUWA BIU: Yadda matafiya ke cin kwakwa Tsawon shekaru 9 an kasa kammala gyaran titin kilomita 125
  • KARKATAR DA NAIRA MILIYAN 289: EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Katsina a kotu
  • DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.