Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana rahoton damke wasu mutane 17 da ake zargin su da ayyukan kungiyar asiri a yankunan Gwagwalada, Gwagwa, Lugbe da Kuruduma.
Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan FCT, Meriam Yusuf, ta fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi a Abuja.
Ta yi karin hasken cewa damke masu ayyukan asirin na daga cikin wani kokari da jami’an tsaron FCT ke yi domin kakkabe Abuja da kewayen ta daga masu ayyukan laifuka manya da kanana.
Meriam ta ce an damke su tsakanin ranakun 5 zuwa 9 Ga Afrilu, kuma jami’an yaki da masu ayyukan asiri na rundunar ‘yan sandan ne su ka kama su a wani samame da suka rika kai masu.
“Wadanda ake zargin sun amsa da kan su cewa su na cikin kungiyar asiri ta Vikings da Aro Baga, wadanda su ka addabi mazauna yankin da fitintinu.
Kuma ta ce wasu hujjoji da aka samu tare da su, har da bindiga kirar ‘pistol’ da albarusai da zabga-zabgan wukake, gatari da adduna da kuma ganyen taba wiwi da guraye, karhuna da sauran tarkacen tsatsube-tsatsube.
Sannan ta ce za a gurfanar da su kotu da zaran an kammala binciken da ake yi masu.
A karshe ta roki jama’a su rika sanar da hukuma da zarar sun ga wasu bakin ido a yankin su, wadanda ba su aminta da irin ayyukan da su ke yudanarwa ba.
Sai ta bayar da lambobin wayar da za a kira idan ana bukatar jami’an tsaro su kai dauki da gaggawa a wani wurin da ake aikata laifuka: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da kuma 08028940883.
Ta kuma yi kira da a rika kai rahoton jami’an ‘yan sandan da su ka nemi wuce-gona-da-iri ta hanyar kiran wannan lamba ga Hukumar Kai Korafe-korafe: 09022222352.
Discussion about this post