Sunan mutum na iya kasancewa a jerin sunayen wadanda Amurka ke sanyawa ido bisa zarginsu da ta’adanci (Watchlist) ba tare da mutum ya sani ba. Ga bayani dangane da yadda akan sami hakan da ma dalilan da ke janyowa:
Wani rahoto ya ce Amurka na iya sanya sunar mutum a jerin sunayen wadanda take zargi da ta’adanci ba tare da ya sani ba. Amma kar ku damu wannan rahoton Dubawan zai baiyana muku yadda za ku san ko hakan ya shafe ku, abun da hakan ke nufi da ma yadda zaku iya cire kanku daga wannan jerin sunaye.
Labarin kasancewar sunan ministan sadarwar Najeriya Isa Pantami a cikin jerin sunayen
Kwanan nan ne kafofin yada labarai suka cika da rahotannin cewa gwamnatin Amirka ta sanya sunar ministan sadarwar Najeriya, Isa Pantami a jerin sunayan wadanda take zargi da ta’addanci inda ta ce yana da dangantaka da Boko Haram.
Rahoton wanda aka wallafa a kafofi da shafukan labarai daban-daban kamar News Wire da Independent Nigeria, ya kuma dauki hankali a shafukan sada zumunta musamman Twitter.
Rahotannin na zargin cewa Mr, Pantami wanda mallamin addinin musulunci ne ya yi abota da tsohon shugaban kungiyar Boko Haram wato marigayi Yusuf Mohammed da ma shugaban kungiyar Al – Ka’ida wanda ya yabawa a wasu daga cikin hudubobin shi. Rahoton ya kuma yi zargin cewa ministan ya sami horoswa a Saudiyya da yankin Gabas ta Tsakiya tare da wasu manyan malaman jihadi.
Shafin Twitter ne ya kasance dandalin zazzafar mahawara dangane da batun na Pantami. Masu amfani da shafin da dama sun yi ta sukar ministan suna kiran shi dan ta’adda, Boko Haram, mai ra’ayin Al-Ka’ida har ma ya kai ga kiraye-kirayen da ya yi murabus. Kiraye-kiryen ya dauki hankali sosai inda aka rika amfani da #pantamiresign dan yin kiran.
Mr. Pantami ya fito ya karyata wannan zargi ya ma yi barazanar cewa zai kai batun kotu sa’annan ya bukaci wadanda suka wallafa rahoton su janye.
Sa’o’i kadan barazanar ta sa, News Wire da News Blog, kafofin labaran da suka fara fitar da rahoton da ya janyo cece-kucen suka janye rahoton suka kuma baiwa ministan hakuri.
Yayin da take mayar da martini kan rahoton ofishin bincike na tarayya ta Amurka wato FBI ba ta amince da labarin ba illa cewa ta yi “Mungode da kuka tuntube mu sai dai bisa manufofinmu ba za mu iya amincewa ko karyata batun ko sunan mutun na cikin jerin sunayen wadanda muke zargi ‘yan ta’adda ne ba,” amsar da FBI ta baiwa jaridar Leeadership ke nan bayan da ta yi masu wannan tambayar.
Mene ne Watchlist kuma ta yaya sunan mutun ke shiga?
US Watchlist wani jadawali ne da Amurka ke da shi na tantance wadanda ta ke zargi ‘yan ta’adda ne. Nan ne kuma take ajiye bayanan sirri da na tsaro dangane da mutane ko kuma kungiyoyin da ake kyautata zaton suna taimakawa wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci.
A shekarar 2003 gwamnatin Amurkan ta fara ajiye Watchlist a matsayin martani ga hare-haren da aka kai mata ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 wanda ya kai ga mutuwa da jikkatan dubban mutane da asarar dukiyoyin da suka kai biliyoyin dala. Yana samar da cikakkun bayanai dangane da ‘yan ta’adda dan jami’an tsaro na tarayya da jihohi da kananan hukumomin Amirka da ma hukumomin tsaron cikin gida na tarayya da jihohi su yi amfani da su. Cibiyar tantance ‘yan ta’adda wato TSC, wanda ke karkashin FBI ce ke daukar nauyin hada wannan jerin sunaye.
Mutum na iya gano sunan shi a jerin sunayen ta yin amfani da ranar haihuwa, lambar da ke jikin fasfo, zanen yatsu, da ma lambobin da TSC ko kuma wasu hukumomin gwamnatin suka baiwa mutun a jadawalin sunayen.
Mutun na iya kasasncewa a watchlist idan har ya taba ma’amala da kungiyoyin ‘yan ta’adda, ko kuma ana zargin shi da taimakawa ko kuma baiwa kungiyoyin ta’adda kudi su gudanar da ayyukan ta’addanci a kan Amurka da yankunanta da ma sauran kasashen duniya.
Ta yaya Amurka ke samun bayanan mutanen da take sa wa watchlist
Tana samun bayanan ne daga jama’a, hukumomi, kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke yaki da ta’addanci, jami’an tsaro, hukumomin da ke ajiye bayanan siri, gwamnati da bayanan da gwamnatocin kasashen waje ke da shi kan al’ummominsu.
Domin samun bayanan wadanda ba ‘yan kasa ba, akwai wani shiri na musamman wanda ake kira shirin kariya da yaki da miyagin laifuka (PCSC) wanda ya baiwa Amurka damar samun bayanan jama’a daga kasashen da ke kawance da ita a karkashin shirin.
Haka nan kuma, Amurkar ta bukaci Najeriya da sauran kasashen da ke hada kai da ita wajen yaki da ta’addanci su bayar da bayanan duk masu aikata miyagin laifuka da ta’adanci. Wannan shi kuma yana karkashin wani shiri na daban wanda ya tanadi cewa duk kasashen da suke da wannan ma’amala da Amurka ba zasu tanadi biza ko izini kafin su shiga kasar idan har suna ba ta wadannan bayanan.
Kasar na kuma iya samun bayanai daga gwamnatocin kasashen duniya a karkashin shirin musayar bayanan jama’a wanda ya kunshi hoton fiska, zanen yatsa da sauran abubuwan da ke nuna siffa, asali da yanayin rayuwa ko zamantakewar mutun. Da wannan shirin, Amurka sa samun bayanai masu inganci sosai daga jami’an tsaron kasashen da ke wannan hadakar da ita. Yawancin bayanan, na mutanen da kasashen ketare, da Amurka, da al’ummar tsaro ta kasa da kasa ke zargi da ta’addanci ne. Haka nan kuma yawancinsu ana danganta su da ayyukan ta’adanci ko miyagun laifuka ko kuma aikata miyagun laifuka a kasashe da dama.
Wata hanya kuma ita ce amfani da na’urar karbar zanen yatsotsi wanda ma’aikata ke amfani da ita su ajiye bayanan jama’a. Suna iya yin haka da wayoyin hannu ko kananan kwamfutocin da FBI ke bayarwa. Wannan kan taimakawa FBI wajen tantance duk wadanda ake zargi da kasancewa ‘yan ta’adda nan da nan, a ciki da wajen Amurka.
Yaya sunan mutum ke kasancewa a watchlist?
Akan gudanar da zabe kafin sunan mutun ya shiga watchlist. Hukumomin gwamnatin Amurka za su zabi mutanen da suke ganin sun cancanci kasancewa a watchlist din. Yawanci wadanda ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne, ana yin haka ne bisa bayanan sirrin da aka samu daga jami’an tsaron cikin gida, da hukumomin tsaro da al’ummar jami’an leken asiri da jami’an ofisohsin jakadancin Amurka.
Kowani ofishi ko hukuma zai tura sunayen da ya zaba zuwa cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa wato NCTC wadda za ta tantance sahihancin bayanan. Daga nan sai a shigar da su manhajan da ke tantance wadanda ake zato ‘yan ta’adda ne kafin a tura sunayen zuwa cibiyar tantancewa ta TSC. Ita kuma TSC sai ta sake gudanar da wani binciken dan ta sake tantance bayanan da aka bata tana kwatantawa da wanda take da shi a baya.
Dalilan da suka sa mutum zai iya kasancewa a watchlist ba tare da saninsa ba.
Mutane na iya kasancewa kan wannan jadawalin ba tare da sun sani ba domin irin wadannan takardun ana ajiye su a matsayin sirri, ba kowa ne zai iya gani ba sai wanda aka tantance. A cewar FBI duk wani abun da ke cikin watchlist ba wanda zai iya gani ko gyarawa bisa tanadin sassan (j) da (k) a dokar sirrin kasar (Privacy Act) domin suna dauke da bayanan sirri da dokokin tsaron da suka danganci shirye-shiryen yaki da ta’addanci, tsaro da leken asirin kasar.
A kan dauki shekaru 99 ana ajiye da bayanan mutanen da ke kan watchlist, bayan nan kuma ana iya sake ajiye su na tsawon wasu shekaru 50 kafin a goge. Idan har an yi ma’amala da wadanda ke kan watchlist din, su ma rahotannin ma’amalar za’a ajiye su na tsawon shekaru 99.
Me kasancewar mutun a kan watchlist ke nufi?
Kasancewar mutun a kan watchlist na iya janyo munanan matsaloli. Na farko dai duk wanda sunansa ya kasance cikin wannan jerin sunayen an haramta masa shiga Amurka ta sama, ta teku da kasa. Haka nan kuma idan har ya yi tafiya za a rika gudunar da bincike a duk kasar da ya shiga ana amfani da tsauraran matakai kamar tsarewa, da amsa tambayoyi daga jami’an Amurka da sauran kasashe a matsayin wanda a ke zargi da ta’addanci. Jami’an tsaron Amurka kuma na iya cafke mutun ta tsare da zarar na’urarsu ta sanar da su cewa mutumin/matafiyin na daya daga cikin wadanda ake zargi da ta’addanci.
Duk wanda ke kan watchlist din kuma ba zai iya samun biza ko izinin shiga Amurka da yankunanta ba, hatta wasu kasashen ketaren da ke kawance da ita. Za’a haramta musu tafiya zuwa Amurka da yankunanta da ma shiga jiragen sama da na ruwan da za su ketara zuwa yankunan Amurka ko ta sama ko ta ruwa.
Bincike da tantance mutanen da ke Watchlist
Umurnin fadan shugaban kasa ga jami’an tsaron cikin gida wanda aka sanyawa hannu ranar 16 ga watan satumbar 2003 ne mafarin kafa cibiyar tantance ‘yan ta’adda ta TSC tare da basu ikon gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana kuma kwanaki bakwai a mako.
TSC ta hada da jami’an ofisoshin jakadanci da jami’an leken asiri da gamayyar hukumomin binciken kan iyaka da masu tantance wadanda aka hana tafiya da miyagin kungiyoyi da kungiyoyin ta’adda.
Duk wani bayanin da ke kan watchlist, jami’an tsaro da na leken asirin Amurka na iya amfani da shi a ciki da wajen kasar a duk sadda suka gamu da mutane yayin da suke gudanar da aikinsu. Misali jami’an kwastam da na kare iyakoki wadanda ke hanyoyin shiga Amirka kan duba watchlist din ne su san ko za su iya barin mutun ya shiga Amurka. Jami’an leken asirin da ke ofisoshin jakadancin Amirka ma kan duba watchlist din kafin su bayar da bisa.
Da zarar aka sami sunan mutun a cikin watchlist din, nan take za’a sanar da TSC wanda su kuma za su bada shawarar irin matakan da za’a dauka dan cigaba da bincike.
A cewar wani rahoto daga wata zaman (110-84) da aka yi a majalisar Amurka a shekara ta 2007. Watchlist na dauke da bayanai 725,442 na mutane 300,000 kuma kowani wata akan sami karin fiye da 20,000. Bisa la’akari da haka, yana iya yiwuwa cewa bayanan sun kai miliyan 3.2 a watan Afrilun 2021.
Akwai yadda mutun zai iya cire sunan shi daga Watchlist?
Kasancewa a watchlist abu ne mai matsalar gaske wanda yake sanya mutane a cikin mawuyacin hali. Mutanen da suka yi imanin cewa an basu bayanan karya ko kuma ba’a yi musu adalci ba suna iya zuwa neman gyara a wani shiri na matafiya da ke neman gyara, wanda ake wa lakabi da TRIP. Wannan shiri yana baiwa matafiya damar samun bayani dangane da sakamakon bincike da tantancewar da aka yi musu, daga nan sai su nemi gyara.
Ana kuma iya turaduk wani korafi zuwa jami’an tsaron cikin gida ta shafinsu na yanar gizo, ko kuma email ko akwatin gidan waya. Za’a duba tambayoyin na su a tantance iya kokarin yadda za a iya sannan a tura su zuwa hukumomin da suka dace domin ganin an dauki matakan da suka wajaba.
Da zarar aka gyara, duk wani batun da ya danganci sunan wanda aka a haramtawa tafiya za a tura ga hukumar tsaro na sufuri wato TSA dan a goge sunan daga jerin sunayen da riga aka turawa jiragen sama. A kan iyakoki ma za a sanar da jami’an dangane da batun sauyin matsayin. Sa’annan za a gyara duk wata na’urar da aka saita dan sanar da jami’ai cewa kana kan