Kungiyar Kiristocin Najeriya, yan’uwa da makusantan marigayi tsohon gwamnan Kaduna Patrick Yakowa sun karyata wata takarda da wasu jaridun kasarnan ke yadawa wai Pantami ya jagoranci wani ganawa da kungiyar Jama’atu ta yi a shekarar 2010 a Bauchi da wai a wannan taro ne wanda shi Pantami ya jagoranta aka shirya yadda za a kashe tsohon gwamnan Kaduna Patrick Yakowa.
Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Kaduna John Hayab, ya soki wadanda ke yada wannan takardar karya cewa babu irin wannan magana kuma ba su tare da wadanda suke yada wannan takarda.
” A wannan lokaci da kowa a wuya yake, yada irin wadannan takardu ba zai haifar wa kasa da alkhairi ba. Dole jami’an tsaro su shiga cikin wannan magana da wuri-wuri tun kafin a yi da na sani akai.
” Mu yan uwan marigayi Yakowa, ba mu son a dauko magana irin haka wanda ba a yi ba tun da ya rasu shekara 9 kenan. A tada mana da hankali a saka mana damuwa a zuciya. Idan abu irin haka ya taso ba a shafukan yada labarai za saka ana wasa da shi ba a bu ne mai mahimmanci da jami’an tsaro dole su shiga ciki.
CAN ta ce da ganin irin wannan takarda ya nuna akwai coge da abin tambaya akai.
Haka ita ma kungiyar Koli ta addinin musulunci ta karyata wannan magana da takarda sannan ta ce ko yadda aka rubuta takardar ya tabbatar ba kungiyar bace ta rubuta shi.
” Akwai yadda takar dai da kira malaman mu, sannan abu mafi muhimmanci da ya kamata a sani shine, Pantami bai taba zama dan kungiyar Jama’atu ba, har kwanan gobe.
Wadanda suka kirkiro wannan takarda sun shirga karya ne kawai domin wata manufa ta su.