Duk da wasu mazauna Geidam dake jihar Yobe sun shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa har yanzu ana jin karar harbin bindiga na batakashi tsakanin sojojin Najeriya da Boko Haram, wannan karon Boko Haram ba su sha da dadi ba.
Sojojin sama sun rika yi wa Boko Haram aman bama-bama daga sama, na kasa kuma suna ragargazar su da bindiga, duk sun fita hayacinsu, daga nan sai suka watsa takardu da ke kunshe da sako.
Mazuna sun ce ‘Yan ta’ addan sun yada zango a wata makarantar Firamare da ke unguwar Hausari, inda daga nan ne suke kai hari ga sojojin Najeriya.
Maharan sun barnata, wurare da dama har da tashar sadarwar dake garin duk sun lalata.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin harin da Boko Haram suka kai a garin Geidam, mahaifar sabon Sufeto janar din ‘Yan sanda Alkali.
Wakilin PREMIUM TIMES ya rika jin rugugin manyan bindigogi a cikin garin, lokacin da ya ke waya da wani mazaunin cikin garin.
“Yanzu ba zan iya magana ba, domin na tabbatar ka na jin karar manyan bindigogi na tashi. Mu yi magana idan komai ya lafa..” Haka wannan mazaunin Giedam ya fada a cikin tsananin firgici.
A ranar 9 Ga Fabrairu, 2021 Boko Haram sun kai farmaki a Girdam, kwana daya bayan ziyarar da sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Ibrahim Attahiru ya kai wa sojoji ziyara a garin.
Kakakin yada labarai na :yan sandan Jihar Yobe Dungus Abdulkarim ya nemi wakilin ya ba shi lokacin da zai binciki lamarin kafin ya waiwaye shi.