TALLAFIN RAMADAN: Yadda Dan Majalisar Daura ya yi wa limamai, malamai, hakimai, jami’an tsaro da ‘yan siyasar Daura watandar naira miliyan 6.3

0

A ci gaba da tallafa wa masara galihu a ake yi lokacin azumi, wajen tallafa masu da abinci da kudade, a ranar Juma’a, 23 Ga Afrilu, 2021, Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Daura, Nasir Yahaya ya kaddamar da rabon tallafin kudi a harabar ofishin sa da ke Daura.

Kudin wadanda yawan su ya kai Naira miliyan 6,345,000.00, an kasafta ta su kamar haka:

1) Shuwagabannin APC Exco na Karamar Hukumar Daura an ba su Naira 1,620,000.

2) Masu Ruwa da Tsaki na jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Daura (Stockeholders). N370,000.

3) Hakimai da Dagatai na Karamar Hukumar Daura N195,000.

4) Malaman Addini na Karamar Hukumar Daura, N250,000.

5) Limaman Juma’a na Karamar Hukumar Daura N150,000.

6) Marayu na Karamar Hukumar Daura N500,000.

7) Kwamitin Yakin Neman Zabe na Dan Majalisar N450,000.

8) Masu Amfani da Kafar Sadarwa (Social Media) N400,000.

9) Jami’an Tsaro (Security) N110,000.

10) ‘Yan Nasiriyya N300,000.

11) Sauran Alummar Gari N2,000,000.

Wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Honorabul Yahaya, mai suna Rabe Arma ya fitar kuma aka watsa a Katsina, ya bayyana cewa da ya ke gabatar da jawabin, sa bayan da ya kaddamar da rabon tallafin kudin, Nasir ya yi godiya ga Allah wanda da ikon sa ne ya sa ya kaddamar da wannan tallafi.

Ya kara da cewa ya bayar da wannan tallafin ne albarkacin wannan wata da ake ciki na Ramadan.

Ya ce tallafin zai saukaka wajen samun sauki ga al’umma.

Shi ma a na sa jawabin, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Shiyyar Daura, Usman OC, ya yaba da wannan abin alheri da Dan Majalisa ya yi.

Ya ja hankalin ‘ya’yan jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Daura da su kara hada kan su domin ciyar da al’umma gaba.

Share.

game da Author