Shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN), bayyana cewa za su fito a fadin kasar nan baki daya su yi zanga-zanga a ranar 19 Ga Afrilu, 2021.
Sun bayyana wannan sanarwa ce bayan sun shafe mako daya su na garkame da kotunan Najeriya, sun hana a gudanar da shari’u.
Wannan barazanar shirya zanga-zanga ta na kunshe cikin wata takardar da ta fada hannun manema labarai a Lagos, wadda aka sa wa hannu a ranar Juma’a, 16 Ga Afrilu, 2021.
Mataimakin Sakataren Kunguyar JUSUN, P. Nnamani ne ya sa wa takardar bayar da umarnin fitowa yin zanga-zanga, bayan an kwashe kwanaki 11 su na yajin aikin da ya gurgunta hankokin shari’u, ya haifar da cinkoso a gidajen kurkuku.
Gaba dayan mambobin JUSUN sun tafi yajin aiki tun a ranar 6 Ga Afrilu, inda su ke neman a bai wa kotunan kasar nan cin gashin kan su.
Sun kuma bada umarnin a ci gaba da zaman yajin aiki, har sai ranar da aka biya masu bukatun su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Majalisar Tarayya ta roki Kungiyar JUSUN su daure su koma bakin aiki, su daina dukan Gwamnatin Tarayya a kan laifin da Gwamnatocin Johohi su ka kantara masu.
JUSUN ta bada sanarwar cewa ta na umarnin dukkan mambobin ta na kasa baki daya, su fito a jihohin su domin su yi zanga-zanga a ranar Litinin, 19 Ga Afrilu.
“Mu na sanar da dukkan mambobin JUSUN na kasa baki daya cewa, bayan tashi daga taron da Kwamitin Gudanarwa na JUSUN ya yi a ranar 15 Ga Afrilu, 2021, an amince cewa za a shirya gagarimar zanga-zanga a ranar 19 Ga Afrilu.
“Za a gudanar da wannan zanga-zanga a kowace jiha da Babban Birnin Tarayya Abuja. Kuma a lokuta daya za a hudanar da zu.
Dalilin Zanga-zanga:
Babban Jami’i na Kasa na JUSUN, Jimoh Musa, wanda ya ke Shugaban Riko na Kungiyar, tun bayan tafiyar Shugaban Kungiyar jiyyar wasu raunuka da ya ji bayan ya yi hatsarin mota, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Ministan Kwadago Chris Ngige ya bata masu rai a taron kokarin sulhun da ya dage katsahan, babu rana, babu lokacin sake zaman.
“To kuma dama mun yanke shawarar cewa idan dai ba mu ji komai ba daga bangaren Gwamnatin Tarayya har zuwa ranar Litinin, to fa za mu hada wannan yajin aiki da fitowa mu yin zanga-zanga kawai.
Ya ce a Abuja dai JUSUN za su fito su yi jerin gwano zuwa Ofishin Akanta Janar na Tarayya, wanda shi ne Ma’ajin Baitil Malin Najeriya, ofishin da ake kira TREASURY HOUSE da kuma Ofishin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami.