‘Yan sandan Kano sun Kama mutumin dake siyar wa mahara babura a Zamfara

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama mutumin dake siyar wa mahara babura a jihar Zamfara.

Kiyawa ya fadi haka ne da yake ganawa da BBC Hausa ranar Talata a garin Kano.

Ya ce rundunar ta samu labarin kasuwancin da yake yi da maharan daga wajen ‘yan kasuwa dake siyar da babura a jihar Kano.

“Mun kama mutumin a hanyar sa ta zuwa jihar Zamfara zai je kai babura biyu da maharan suka siya a hannun sa.

Kiyawa ya ce mutumin ya tabbatar wa ‘yan sandan cewa ya siyar wa maharan babura kira Honda ACE 125 sama da 100 akan Naira 600,000.

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka yi wa wani jagoran fulani Lawal Maijama’a, kisan gilla a karamar hukumar Kauru, jihar Kaduna ranar Lahadi.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan wanda ya sanar da haka ya ce a bayanan da jami’an tsaro suka yi maharan sun afka wa Alhaji Lawal Musa wanda aka fi sani da Maijama’a a hanyarsa ta dawo wa gida a tsakanin yankin tare da yayan sa.

Bayan sun harbe shi maharan sun tsarge wuyar sa har sai da suka ga ba ya numfashi, sannan suka jefar da gangan jikinsa suka kama gabansu.

Aruwan ya ce gwamnatin Kaduna na jimamin kisan Lawai Maijama’a domin yana daga cikin wadanda ke kokarin matuka na ganin an samu zaman lafiya a wannan yanki.

Share.

game da Author