Akalla mutum 122,000 ne su ka kai kan su aka yi masu allurar rigakafin korona, samfurin AstraZeneca a Najeriya.
Shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA), Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka a taron da kwamitin PTF ta yi da manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Ya ce har yanzu babu wani rahoton samun matsala ko da daya ne a kasar nan da aka fara yi wa mutane rigakafin korona.
Shu’aib ya yi kira ga yan Najeriya musamman masu fama da wasu cututtuka wanda ba Korona ba su garzayo wuraren da ake yin rigakafin Korona ayi musu.
Idan ba a manta ba a ranar 16 ga Maris ne Shu’aib ya bayyana cewa an yi wa mutum 8,000 allurar rigakafin korona a kasar nan.
Shugaban hukumar NPHCDA ya ce hukumar za ta yi kafada-da-kafada da Hukumar NAFDAC domin sa-ido kan allurar da kuwa wadanda ake wa allurar, domin ganin ko da za a samu wani rahoton wanda ya fuskanci wata matsala.
An kawo akalla kwalaben rigakafin AstraZeneca guda milyan 4 a Najeriya.
Shugaban kwamitin PTF Boss Mustapha ya ce kamfanin MTN ta kawo wa Najeriya kwalaban maganin rigakafin cutar 300,000 ranar Lahadi.
Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da yin allurar ta AstraZeneca a Najeriya, wasu kasashe da su ka hada da Jamus, Italy, Faransa, Netherlands, Ireland, Austria, Afrika ta Kudu da sauran kasashe da dama irin sun dakatar da yi wa al’ummar kasashen su rigakafin AstraZeneca, biyo bayan rahotannin cewa allurar na haddasa toshewar magudanan jini a cikin jikin wanda aka yi wa allurar.
Bayan haka Shu’aib ya ce gwamnati ta raba wa duk jihohin kasar nan maganin rigakafin banda jihar Kogi.
Ya ce jihar Kogi bata karbi maganin rigakafin ba saboda rashin samar da wuraren ajiye maganin rigakafin da daukan ma’aikatan da za su yi wa mutane allurar rigakafin.
Discussion about this post