“Rabon da na sa shi ido ko na ji muryar sa, tun a ranar 2 Ga Janairu, 2009, ranar da na kai masa abinci a Ofishin ’Yan Sanda na Kuje, Abuja.”
Wata mai bayar da shaidar irin cin zarafin da ake zargin jami’an ’yan sanda na aikatawa, wanda sanadiyyar ire-iren su ne matasa su ka harzuka, har su ka yi zanga-zangar #EndSARS, ta bayyana yadda dan’uwan ta mai suna Jude Onunze ya salwanta a hannun jami’an ’yan sanda a Kuje, Abuja sama da shekaru 12 da su ka gabata.
Ms Okwor, wadda ta bayyana a gaban kwamitin binciken zarge-zargen t ake hakkin jama’a da ake yi wa jami’an ‘yan sanda, ta bayyana wa kwamitin cewa an kama dan’uwan ta a ranar 1 Ga Janairu, 2009, bayan da wani abokin sa ya kai kara cewa ya doke shi.
“Rabon da na sa shi ido ko na ji muryar sa, tun a ranar 2 Ga Janairu, 2009, ranar da na kai masa abinci a Ofishin ’Yan Sanda na Kuje, Abuja.”
Takardar Korafi: Matar ta bayyana a gaban kwamitin domin yin karin haske kan wata takardar korafin da iyalan su su ka mika wa kwamitin, domin a bi masu hakkin su a hannun jami’an ‘yan sanda, a tilasta su fito masu da dan’uwan na su idan ya na da rai.
Kwamitin wanda ke karkashin tsohon Mai Shari’a na Kotun Koli, Suleiman Galadima, an kafa shi ne a karkashin Hukumar Kare Hakkin Jama’a ta Kasa a fadin kasar nan, biyo bayan mummunar tarzomar da aka yi a fadin kasar nan kan take hakkin jama’a da jami’an SARS ke yi, tare da sauran cin zarafin jama’a da aka dade ana zargin ‘yan sanda na aikatawa.
Wannan zaman sauraren kara dai an yi shi ne a ranar Laraba, kuma Hukumar NHRC ce ta turo wa PREMIUM TIMES HAUSA yadda zaman kotun ya wakana.
Matar ta yi karin hasken cewa bayan an kama dan’uwan na ta, ya kira ta a waya ya sanar da ita cewa an kai shi ofishin ‘yan sanda na Kuje, a ranar 1 Ga Janairu, 2009.
Bayan ta garzaya ta je, sai ta sami jami’in da kokarin ke hannun sa, wanda ya ce mata ta koma washegari.
Ta ce washegari ranar 2 Ga Janairu, ta je ta kai masa abinci, kuma tun daga ranar ba ta kara ganin sa ba.
Daga nan ta ce ta samu damar mika masa abinci a lokacin ya na bayan kanta a tsare, bayan da ta dandana abincin kamar yadda aka umarce ta.
“Ni da miji na da Shugaban Kabilar Ibo na Kuje, Akpata Justice, mun koma ofishin a ranar 4 Ga Janairu, 2009, amma sai jami’in dan sanda mai bincike Peter Ageh ya shaida mana cewa an dauki dan’uwan nawa an maida shi gida a cikin motar sintiri ta ‘yan sanda.
Su na gama jin wannan bayani, sai su ka garzaya gidan dan’uwan na ta, amma su ka samu kofar a rufe, kuma babu wata alama da ke nuni da cewa ya koma gidan.
Ta kara da cewa sai su ka koma ofishin ‘yan sanda su ka shaida masu cewa dan’uwan na su fa ba ya gida.
Ta ce tun daga lokacin har yau babu labari.
“Na je kotu, na je Majalisar Tarayya a kan wannan lamari na bacewar dan’uwa na kafin na kawo kara nan wurin Hukumar NHRC.”
Lauyan ‘yan sanda James Idachaba ya bayyana cewa ai “wannan magana ta na hannun kotu, don haka kotu ta karbi maganar kenan.”
Idachaba ya shaida wa kotu cewa akwai daukaka karar da aka yi, kuma maganar na a gaban Kotun Daukaka Kara.
Amma kuma lauyan masu karar a fito masu da dan’uwan su, Chukwudi Igwe, ya shaida wa kwamitin kotu cewa an dauka Jude ya mutu, don haka bai san da wata maganar sa a gaban kotu ba.
Daga nan aka daga sauraren kara domin a bai wa bangarorin biyu damar komawa Babbar Kotun Abuja ko Kotun Daukaka Kara su gano inda aka kwana dangane da shari’ar salwantar mutumin a hannun ‘yan sanda.