Bulalar Majalisar Dattawa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007, Orji Kalu, ya bayyana cewa ya gode wa Ubangiji da ya kaddare shi zaman kurkuku, sannan ya fito.
Kalu ya bayyana haka a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Umuahia a ranar Talata, inda ya kara da cewa zaman gidan kurkuku da ya yi, wani babban darasi ne ya koya.
Kakakin Yada Labarai na Kalu, mai suna Peter Eze, ya ce sanatan ya yi furucin a wurin kamfen din kanin sa Mascot Kalu, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC na zaben Majalisar Tarayya na Mazabar wakilcin Kananan Hukumomin Aba ta Arewa da ta Kudu, wanda za a yi a ranar 27 Ga Maris.
An dai yanke wa Kalu ne shekaru 12 a gidan kurkuku na Kuje, Abuja a ranar 5 Ga Disamba, 2019, bisa zargin wawurar naira biliyan 7.1, lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Abia, tsakanin 1999 zuwa 2007.
Bayan ya yi zaman watanni shida, Kotun Koli ta soke hukuncin da Mai Shari’a Mohammed Idris na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ya yi masa.
Kotun Koli ta bayyana cewa Mohammed Idris ba shi da ikon yanke wa Kalu hukunci, saboda a lokacin da ya yanke masa hukuncin an rika an kara masa mukami, don haka bai kamata a ce ya na shari’a a Kotun Daukaka Kara a lokacin ba.
“Masu gaba da ni sun dauka zan zama shugaban kasa cikin 2023, shi ya sa su ka yi tunanin datse min rayuwa ta ta kowane hali.
“To amma su wadannan dibgabbun fa ba Ubangiji ba ne su. Sun dauka zan ji kunyar zuwa kurkuku. To ba na jin kunyar zaman da na yi a kurkuku. Kuma ba na kullace da su, saboda ba su san irin kusancin da na ke da shi da ubangiji na ba.
“Annabi Yusuf an kulle shi a kurkuku, shi ma tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo an kulle shi a kurkuku.
“Zama na kurkuku wani bangare ne na rayuwa ta da zan rubuta tarihi na, idan Ubangiji ya ba ni damar wallafawa.”
Discussion about this post