ZABEN 2019: Wanda ya kashe Shugabar Matan PDP a Jihar Kogi zai shekara 12 a kurkuku

0

Babbar Kotun Idah da ke Jihar Kogi ta daure Ocholi Edicha shekaru 12 da watanni shida a gidan kurkuku, bisa samun sa da laifin kashe Solome Abuh, wata shugabar matan jam’iyyar PDP a garin su.

An same shi da laifin fashi da makami, kisa da kuma hada baki a aikata mummunan laifi tare da shi.

A tsawon lokacin da aka shafe na shekaru biyu ana shari’ar, mai gabatar da kara ya kai shaidu biyar a gaban ai shari’a.

Rahoton hukuncin shari’ar ya nuna cewa kotu ta yi amfani da bayanan da masu shaida su ka gabatar da kuma rubutattun bayanan da ‘yan sanda masu bincike da gabatar da kara su ka gabatar wa kotu.

Duk da cewa wanda ake tuhuna din ya musanta cewa shi bai yi wa ‘yan sanda wani bayani sun rubuta ko ya rubuta da kan sa ba, amma kuma ya amince da wani bangare na bayanan ‘yan sandan, wanda aka gabatar wa kotu.

Solome ta gamu da ajalin ta yayin da aka bindige ta a gidan ta, sannan aka banka wa gidan wuta a garin Ochadamu, cikin Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi. A lokacin zaben gwamna a 2019.

Bayan faruwar lamarin ne jami’an ‘yan sanda su ka gabatar da mutum shida a kotu, ciki kuwa har da Edicha.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kogi a lokacin ya bayyana sunayen wadanda aka kama din cewa akwai Ocholi Edicha, Adamu Haruna, Onu Egbunu, Musa Alidu, Attai Haruna Egwu da kuma Attah Ejeh.

Ya ce an kama su tare da taimakon ‘yan bijilanti a ranar 22 Ga Nuwamba, 2019.

Share.

game da Author