RIGAKAFIN KORONA: Abubuwan da wanda aka yi wa allurar ‘Covid-19’ ka iya ji a jikin sa – CDC

0

Duk da an hakkake cewa duk wanda aka yi wa rigakafin kamuwa da cutar korona ya tsallake siradin ta, Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka (CDC) ta bayyana wasu alamomin rashin jin dadin jiki da aka iya kama wanda aka yi wa rigakafin na allurar.

CDC ta ce wadannan alamomin rashin lafiya da mutum zai ji a jikin sa, ba abin damuwa ba ne, domin a lokaci guda kuma jikin wanda aka yi wa allurar rigakafin na ci gaba da gina makaran hana cuta shiga cikin sa.

Cibiyar ta ce abin da mutum zai rika ji na wani lokaci a jikin sa, ka iya hana shi gudanar da wasu ayyukan yau da kullum, amma cikin kwanaki kadan zai wartsake, ya murmure.

Sannan kuma CDC din dai ta kara da cewa wasu mutanen da dama kuma ba lallai ne ma su rika jin wata alamar rashin lafiya a jikin su, bayan an yi masu allurar rigakafin ba.

1 – Dantsen Da Aka Yi Maka Allura: A damtsen da aka yi wa mutum allurar korona, zai rika jin zafi, wurin zai yi ja kuma zai kumbura.

2 – Sauran Sassan Jiki: A dukkan sauran sassan jikin mutum zai rika jin gajiya likis, ciwon kai, ciwon tsokar ciki, tashin tsikar jiki da zazzabi. Haka CDC ta bayyana.

Masana sun ce idan ka ji wadannan ko wasu daga cikin wadannan alamomin, to ka garzaya ko da sahihin kantin sayar da magani ne, ka sayi maganin kashe wadannan ciwo.

Sai dai kuma ba a shan maganin kafin a yi wa mutum rigakafin korona, da nufin wai ya sha maganin don kada ya ji wadancan alamomi bayan an yi masa allura.

Wata dabarar rage jin zafin ciwon allurar korona ita ce, da zarar an yi maka ita, to nan take ka samu wani tsumma mai tsabta ko wani kyalle, ka wanke shi, a jika shi cikin ruwa mai sanyi kana dan daddanawa a kan damtsen ka, daidai inda aka yi maka allurar rigakafin korona.

Jami’an kula da lafiya na ganin cewa alamomin wadannan rashin lafiya a jikin wanda aka yi wa allurar korona, su na nufin maganin ya na aiki a jikin ka kenan.

Akwai sauran bayanai amma duk da haka, CDC ta ce a ci gaba da rufe hanci da baki da takunkumin kariya, a daina shiga cinkoson jama’a. A rika tsayawa da tazara mai dan nisa da mutum, sannan a ci gaba da wanke hannaye.

Share.

game da Author