TITIN NAIRA BILYAN 797.23: PDP ta ce akwai rufa-rufa da cuwa-cuwa a sabuwar kwangilar titin Abuja zuwa Kano

0

“Kai jama’a! idan fa aka yarda cewa naira bilyan 797.23 za a kashe ta a titin Abuja zuwa Kano, mai tsawon kilomita 375, kenan za a dagargaje naira bilyan 12.12 a duk kilomita 1 kadai.”

Jam’iyyar PDP ta yi fatali tare kuma da nuna kin yarda cewa gaba dayan naira bilyan 797.23 duk a kan titin Abuja zuwa Kano za a kashe su.

Baya ga cewa kudaden sun yi yawan da ko mahaukaci sai ya yi mamakin yawan adadin kudaden, PDP ta ci gaba da cewa bayyana wadannan kudade a matsayin kudin kwangilar sake titin ya kara fito da irin munin harkalla, badakala, rufa-rufa da cuwa-cuwar da ke ci gaba da gunada a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyar APC.

Wata sanarwa da Kakakin Yada Labrai na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya bayyana cewa, “Jamiyyar PDP ba ta na adawa ko nukura ba ne da irin ayyukan ci gaban da za a yi wa al’umma, musamman aiki mai muhimmanci kamar na titin Abuja zuwa Kaduna har Zariya zuwa Kano. PDP na magana ne a kan mahaukatan kudaden da aka ce wai duk a kan titin za a dagargaje su.

“PDP da duk wani dan Najeriya na mamakin irin makudan kudaden da aka ce za a kashe wajen sake gina wannan titi, wanda hankali da maras hankali ba zai iya amincewa da yawan adadin ba.”

Cikin makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta maida aikin titin daga gyare-gyaren da za a kashe naira bilyan 155 a kammala, ta bayyana cewa yanzu kuma bambare titin za a yi baki dayan sa, a sake sabo rangadau, amma kuma za a dagargaje har naira bilyan 797.23 a aikin sake gina titi, tun daga Abuja har Kano.

“Kai jama’a! idan fa aka yarda cewa naira bilyan 797.23 za a kashe ta a titin Abuja zuwa Kano, mai tsawon kilomita 375, kenan za a dagargaje naira bilyan 12.12 a duk kilomita 1 kadai.

A kan haka ne sanarwar da PDP din ta fitar, ta nuna cewa matsayar ta a wannan kwangila shi ne an kirkiro ta ne kawai domin a karkatar da wasu makudan bilyoyin kudaden da ba a san adadin su ba, ta yadda za a sake tsiyata Najeriya, daga matakin tsiyata ta da ake a kan yi yanzu.”

Wannan kwangila dai ’yan Najeriya ba su da labarin cewa za a sake ta, kuma babu wanda ya ga lokacin da aka buga tandar neman‘yan kwangilar za su yi aiki, ballantana a auna cajin kudaden da kowane kamfani ya yi, a san wanda ya cancanta a bai wa aikin.

“PDP na kira ga ‘yan Najeriya su hankalta cewa titin Abuja zuwa Kano mai nisan kilomita 375, wanda za a kashe wa naira bilyan 797.23, kenan fa za a kashe naira bilyan 12.12 ne a kowane kilomila daya.”

Daga nan sai PDP ta bayyana cewa baya ga raina wa ‘yan Najeriya hankali da APC da kuma gwamnatin Buhari ta yi, wannan kwangila ta kara nuna yadda wasu shafaffu da mai ke cin amanar ‘yan Najeriya su na wawurar makudan kudaden talakawa wajen karyar gina titinan da babu mai mai tsarar irin su a fadin kasashen Afrika.

Sannan kuma PDP ta yi zargin cewa a asirce ake bayar da kwangilar, inda jami’an gwamnati ke yin rufa-rufa tsakanin su da ‘yan kwangila.

Akwai kuma zargin cewa wasu ayyukan gwangilar titinan ma ana bayar da su ne tun kafin kamfanin da aka bai wa kwangilar ya mika bayanan adadin kudaden da zai yi cajin a biya shi, kuma tun kafin ya tantance adadin tsawon titin ma dungurugum.

A makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa za a dagargaje naira bilyan 797.2 domin sake titin Abuja zuwa Kano baki dayan sa.

Rahoton dai ya nuna cewa titin Abuja-Kaduna-Kano da yanzu ake kan aikin gyaran wuraren da su ka lalace, yanzu kuma an ajiye batun gyara za a sake titin baki dayan sa.

A kan haka ne Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe zunzurutun kudi naira bilyan 797.2 domin sabunta titin mai nisan sana da kilomita 400.

Minintan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa wannan sabon aiki da za a tattago.

Ya ce an amince da sake titin baki dayan sa ne, a wurin taron Majalisar Zartaswa na Ranar Laraba, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta da kan sa a Fadar Shugaban Kasa.

A wurin taron kuma an amince a sayo motocin kashe gobara da wasu kayyakin da hukumar Kashe Gobara ke bukata.

Fashola ya bayyana cewa aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano da a baya za a kashe wa naira bilyan 155 domin a kammala shi, yanzu zai ci naira bilyan 797.2, domin sabon titi garau za a gina gaba daya.

“Na gabatar da wannan bukata kuma an amince za a sake titin Abuja zuwa Kano gaba dayan sa. Ya tashi daga aikin gyare-gyaren wuraren da su ka lalace zuwa sake gina titin baki daya.

“Kenan kwangilar aikin ta tashi daga naira bilyan 155 ta koma naira bilyan 797.2

“Fashola yace wasu titinan da aka kammala gyarawa kuma nan ba da dadewa ba masu kwangilar za su damka su ga Gwamnatin Tarayya, sun hada da titin Benin-Asaba, Abuja-Lokoja, Kano-Maiduguri, Enugu-Aba, Sagamu-Asaba, Kano-Katsina, Enugu-Fatakwal, Ilorin-Jebba da kuma Lagos-Badagary.

Sai dai kuma Fashola ya ce za a damka wa gwamnati titinan daya bayan daya.

Dangane da titin Abuja zuwa Kano, Fashola ya ce za a fara kammala Kaduna zuwa Zaria mai nisan kilomita 74. Ya ce shi ne za a kammala cikin 2022.

Sai kuma na Zaria zuwa Kano da Kaduna zuwa Abuja ya ce za a kammala shi cikin 2023.

Share.

game da Author