Ciwon murar tsuntsaye mai yi wa dubban kaji kisan farat daya ya bulla a jihar Neja, inda tuni ya haddasa wa masu kiwon kaji asarar kaji masu yawa na miliyoyin nairori.
Gwamnatin Jihar Neja ce ta bayyana bullar cutar a wasu gonakin kiwon kaji a jihar, inda cutar ta kashe kaji masu yawan gaske.
Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Kula da Dabbobi da Kiwon Kifi ta Jihar Neja, Abubakar Kuta ne ya bayyana barkewar murar tsuntsayen a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna, babban birnin Jihar a ranar Alhamis din nan.
Rahotanni sun tabbatar cewa masu kiwon kaji da dama sun tafka asara a fadin jihar sanadiyyar barkewar cutar murar tsuntsayen.
Sanarwar ta kara da cewa dubban kaji sun mutu tare a dibga asarar
milyoyin nairori.
Gwamnatin Jihar ta shawarci masu kiwon kaji su rika kiyayewa da tsafbar gonkin su da filin kiwon su. Sannan kuma su takaita zirga-zirga mutane da motoci a cikin wuraren da su ke kiwon kaji.
Baya kai rahoton bullar cutar da hanzari da aka shawarce su cewa su rika yi, an kuma ja hankalin masu kiwon kaji su rika yi wa garken kiwon kaji feshin magani har ma da kwanukan da su ke zuba wa kajin abinci duk a yi masu feshin magani.
Haka kuma an shawarci masu gonakin su takaita kusantar kajin. Kuma su daina yin musanyar kires na zuba kwai daga wasu gonakin kiwon kiwon kaji ko wurare daban.