Takai, karamar hukumar a jihar Kano, yanki ne Wanda Allah ya albarkata da samun ruwan sama a duk lokacin damina sannan kuma marka-markan filaye da dazuka iya ganinka, a dalilin haka mutanen yankin su ke noma da kiwo da Kuma kasuwanci na faɗa aji.
Garin Takai gari ne Wanda ya yi nesa da birnin Kano da tsawon kilomita 80 Kuma ya yi kusa da yankunan Kasar Bauchi yankin da yake yawan kawowa Kano farmaki a lokacin Sarkin Kano Babba Zaki kamar yadda tarihi ya nuna.
Sanadiyar yawan hare-haren da ake yawan kawowa Birnin Kano, Sarkin Kano Babba Zaki ya yanke shawara a kafa kasar Takai Kuma ayi ganuwa a garin, hakan ne yasa ya turo mayaka domin su zauna a garin.
Bayan an kafa dausayin Yaki a garin Takai, Sarkin Kano Babba Zaki ya Gina gidan Sarkin Kano a garin Takai Kuma ya so ya koma garin da zama.
Dan Sarkin Kano, Abdullahi Maje Karofi, Yusufu ya koma garin Takai da zama lokacin Sarkin Takai Umaru Dan Maisaje.
Kasar Takai ta yi yaki da kasar Ningi a shekara ta 1860-1892 Kuma ta yi nasara akan Kasar Ningi kamar yadda tarihi ya nuna.
Na rubata wannan littafi da nayi wa suna (Takai A Jiya Da Yau) domin hidima ga abun da Shehu Usman Dan Fodiyo ya kafa a kasar Hausa domin samun abun da wadanda za su taso nangaba su karanta abun alkhairin na baya.
Wannan littafi za’a kaddamar da shi nan bada jimawa ba a garin Takai.
Wannan littafin nawa shine littafi na farko da wani dan asalin garin Taki zai rubuta domin karrama garin da fito da ita a idanun duniya.
Domin Karin bayani akan kaddamar da littafin a tuntubi Salihi Garba wannan numbar 08104179801
Discussion about this post