Kotu ta daure ɗan sandan da ya kashe wani matashi a Abuja

0

Kotu dake Nyanya, Abuja ta daure wani ɗan sanda mai suna Johnson Samanja da aka cafke a ka kawo gabanta bisa laifin kisa da yayi.

Bisa ga hukuncin da alkalin kotun Peter Kekemeke ya yanke ranar a farkon wannan mako, ɗan sanda Samanja zai yi zaman kurkukun Kuje Abuja daga yanzu har zuwa 1 ga Yuni.

Kekemeke ya ce a lokacin Samanja zai iya neman a bashi beli.

Lauyan da ya shigar da karan Okokon Udo ya sanar da kotu cewa Samanja ya harbe wannan matashi ranar 3 ga Oktoba 2020 a unguwar Dutse dake Apo.

Sai dai kuma ɗan sanda Samanja ya ƙaryata aikata haka a gaban kotu.

Tuni dai an tasa keyar Samanja zuwa kurkuku zuwa watan Yuni domin a ci gaba da Shari’ar.

Share.

game da Author