Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya koka kan rashin samun hadin kan gwamnonin Arewa don kawo karshen hare-haren yan bindiga a yankin.
Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da rahoto kan matsalolin tsaro da aka yi fama da su a jihar a shekarar 2020.
Rahoton ya kunshi bayanai da kuma nazarin manyan batutuwan tsaro a jihar a shekarar da ta gabata.
” Sam babu dadi karanta abubuwan da wannan rahoton ya kunsa saboda yana tattara ne da bayanan yadda mutane suka jikkita, wasu suka rasa makusantan su da asarar dukiyoyi da aka yi saboda matsalolin tsaro da aka yi fama da shi. Sannan kuma rahoton na kunshe da bayanai kan himma da kokarin da gwamnatin Kaduna ta yi da matakan da ta dauka domin kawo karshen hare-haren yan bindiga a jihar.
” Wasu daga cikin abubuwan da muka yi daga darasin da muka dauka a Zangon farko na mulkin mu shine kirkiro da ma’aikatar tsaro. Wannan ma’aikata ta ke kai koma wajen gano matsalolin da ya kawo mana cikas da bamu shawarwarin yadda za mu tunkare ta.
” Sannan kuma ma’aikatar za ta rika tattaunawa da hada kai da jami’an tsaro domin kawo karshen matsalar tdado a jihar.
Gwamna El-Rufai ya kara da cewa gwambatin jihar na ci gaba da samun hadin kai daga gwamnonin musamman gwamnatun jihar Neja domin gano bakin zaren da kuma fatattakar yan bindiga dake boye a wasu dazuka dake iyaka da jihohin.
Sannan kuma gwamnati ta sassaka na’urorin dauko hotunan mutane domin gano na gari da bata gari wadanda ke hana ruwa gudu a jihar.
Discussion about this post