KILU TA JA BAU: Yadda farashin kayan abinci da nama ke kara tsanani a Lagos, Ibadan da sauran garuruwan kudu

0

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar a garuruwan Lagos, Ibadan, Uyo, Abuja, Benin da sauran garuruwan kudancin Najeriya, ya nuna cewa farashin kayan abinci da naman shanu sai kara tsanani ya ke yi a wadannan garuruwa.

Wannan tashin gwauron zabo da farashin kayan abinci da na naman shanu a kudancin kasar nan, ya faru ne saboda yajin kai kayan abinci da Hadaddiyar Kungiyar Masu Safarar Kayan Abinci da Dillalan Shanu ke yi daga Arewa zuwa Kudu.

Ita dai wannan kungiya ta na neman diyyar naira bilyan 475 a matsayin biyan rayuka da dukiyoyin ‘yan Arewa da su ka salwanta a rikice-rikicen baya-bayan nan da su ka rika faruwa a kudancin kasar nan.

’Yan Lagos Sun Fara Yin Miya Ba Nama:

Wakilin mu da ya ratsa kasuwar Mil 12 da ke Lagos, a ranar Talata, ya lura cewa babu masu sayar da nama, kamar an yi ruwa an dauke.

Sannan kuma tattasai da tumatir ya yi karanci sosai, haka ma kayan abincin da akasari daga Arewa ake kai su Lagos.

A wurare kalilan da ake sayar da tumatir da tattasai a kasuwar, wakilin mu ya tsaya a gefe, ya ga yadda ake wa mai sayar da kayan miya dafifi, saboda karancin kayan.

Sai dai kuma da mai saye ya ji farashi, sai ya dafe kai ya na zare idanu, ya na shafar aljihu. Idan mai saye ya taya, ko albarka ba a ce masa, ballantana a ce kawo kudin. Idan ba ka saye, to ka kara gaba kawai.

Kwandon tumatir din da ake sayarwa naira 5,000 a Kasuwar Mil 12 a kwanakin baya, to a ranar Talata har naira 35,000, saye ko bari.

Haka lamarin ya ke har ga sauran kayan abinci irin su shinkafa da sauran su.

Shi kan sa barkono da attarugu, wakilin mu ya lura farashin su ya fi barkono zafi a ido.

“Ka ga wannan kwandon tumatir din, naira 13,000 zan sayar da shi. Ko saye ko bari, saboda babu shi a kasuwa. Amma kafin wannan matsalar ta faru, naira 2,500 kai har naira 2,000 na sha sayar da kwandon tumatir.”

Haka wani dan tireda ya shaida wa wakilin mu lokacin da ya matsa kusa ya tambaye shi farashi.

Farashin Barkono Ya Fi Barkonon Zafi A Ido:

“Yanzu ka ga farashin barkono ya kai naira 28,000, kamar yadda mu ka sayar da shi jiya Litinin. Amma yanzu yau Talata, idan ka duba kasuwar nan babu barkonon.” Inji wani dan tireda.

Yayin da wakilin mu ya lura cewa babu shanu kwata-kwata a kasuwa kuma babu mahauta a kara, haka ma albasa ta yi tsada, wadda ake sayarwa naira 3,000 a baya, yanzu ta haura naira 25,000.00.

Sai dai wake har yanzu bai kara farashi can sama sosai ba. A yanzu karamin buhu naira 23,000, babba kuma naira 46,000.

A kasuwar doya ta yi karanci, ballantana a rika saye ana kirba sakwara.

Naman Naira 1,500 Ya Koma Naira 8,000 A Uyo, Akwa Ibom:

Kamar Lagos kamar sauran garuruwan kudu. Domin shugaban masu sayar da nama na daya daga cikin kasuwannin Uyo, babban birnin Akwa Ibom, mai suna Mijin Yawa, ya shaida wa wakilin mu cewa babu shanunma ballantana a samu wadda za a yanka a sayar da nama. Wadanda ke akwai sun yi karanci sosai, abin ba a magana.

Ya kara da cewa nama ya yi tsada sosai. A baya har shanu 50 su ke yankawa a rana daya. Amma yanzu ya ce abin yay i wahala sosai. Tun ana yanka 20 a rana daya, har abin na neman gagara.

“A yanzu mu na dan fito da wanda mu ka dan tanada ne domin kada a zo nema babu. Wanda mu ke aunawa a kan sikeli naira 1,500 a baya, to a yanzu naira 8,000 yake.” Inji Mijinyawa.

Saniyar Naira 180 Ta Koma Naira 350 A Benin:

Wani mai suna Tirmidhiy Alamu, ya shaida wa wakilin mu cewa yanzu a Benin, Babban Birnin Jihar Edo, cin nama wai wane dan wane jikan wane. Domin shanun da ke kasa ba su da yawa, kuma sun yi tsada.

Ya ce saniyar da ba ta wuce naira 180,000 ba a kwanakin baya, yanzu haka sai ta kaib naira 350,000 ko sama da haka.

A Abuja ma a Kasuwar Dutsen Alhaji, saniyar 250,000 yanzu ta haura naira 400,000.

Dukkan garuruwan kudu kowace kasuwanni jama’a sai kukan tsadar kayan abnci da nama su ke yi.

Share.

game da Author