Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana wa manema labarai cewa mahara sun Kashe mutum 6 a wasu hare-hare da suka kai kauyukan kananan hukumomin Kauru da Igabi.
Sanarwar wanda wanda kwamishina Aruwan ya saka wa hannu ranar Talata ya ce an kashe mutum daya a hanyar Birnin Yero-Tami, mutum daya kuma ya arce dauke da rauni.Yana asibiti ana duba shi.
” An kashe mutum biyu a kauyen Gwada da wasu mutum biyu a Unguwar Kure duk a karamar hukumar Igabi.
” An kashe wani mutum daya mai suna ‘Likita’ a kauyen Amawan Dadi Rugan Jauru dake karamar Kauru.
A karshe gwamna Nasir El-Rufai ya mika jaje da ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda aka kashe, sannan kuma yayi addu’ar Allah ya ba wadanda suka kwance asibiti lafiya.