Gwamnatin Tarayya ta fara sayar da samfarerar shinkafa tan 200,000 ga masu masana’antun casar shinkafa

0

A karkashin Shirin Bayar da Lamuni ga Manoma na Anchor Borrowers’ Programme, Gwamnatin Tarayya za ta fara sayar da samfarerar shinkafa tan 200,000 ga masana’antun casar da shinkafa 18 a kasar nan.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ranar Talata, a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

“Wato kamar yadda mu ke bayar da kudi ga manoma a karkashin shirin “Anchor Borrowers’ Programme (ABP), to haka za mu fadada wannan lamuni har ga masu masana’antun casar shinkafa.” Inji Gwamnan CBN.

“Za mu rika bayar da lamunin ga masu casar shinkafa, su kuma su rika biyan manoman shnkafa kudin shinkafar su. Su kuma manoman shinkafa, sai su rika biyan CBN lamunin da su ka karba don yin noma.

Bankin CBN ya kara da cewa sun bayar da kudade ga kananan manoma su 2,923,937, wadanda ke noma kayan gona iri daban daban har 23.

Emiefile y ace darasin da aka dauko kuma aka koya daga 2015, shi ne ya sa aka kara bada himma da kuma kara habbaka shirin bayar da kudaden.

Daga nan kuma sai gwamnan na CBN ya rika baya bayanin irin gagarimar nasarar da aka samu a fannin noma ta hanyar Shirin ABP, da ake bayar da lamuni ga kananan manoma.

“Nan ba da dadewa b harkar noma za ta koma hanyar samun makudan kudade ga dukkan manoma, saboda wadanda ke karbar lamuni su na yin noma, yanzu sai cin riba su ke yi a cikin farin ciki.

“CBN mun bayar da kudade ga mambobin Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) har su 221,450 a daminar 2020, cikin jihohi 32.

“Amma ya kamata a sani akwai matukar bukatar duk wanda aka bai wa bashin nan, to ana so fa ya biya, domin shirin ya dore sosai.

Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya bayyana cewa ya na da yakini manoman kasar nan za su fitar da Najeriya daga cikin kalubalen matsin tattalin arzikin da ta ke ciki.

Share.

game da Author