Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Edo, ta bayyana cewa hukumar tsaron a karkashin sa sun sasanta rikice-rikicen makiyaya da manoma har fiye da 50 a fadin jihar.
Ya ce NSCDC ta bayar da horo na musamman ga jami’an ta su 40 domin kwarewa da gogewa wajen sasanta rigingimu da shiga tsakanin bangarori biyu masu tankiya, tun kafin rikicin ya kai ga kisa ko zubar da jini.
Haka nan kuma wannan Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Edo, ta bayyana cewa ta kama masu laifuka daban-daban har 38 a cikin makonni 10.
Babban Kwamandan NSCDC na Jihar Edo, George Edem ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Benin, a babban birnin jihar, yayin da ya ke bayyana irin nasarorin da hukumar tsaron ta samu.
Ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargi da aikata laifukan daban-daban kama daga masu hakar ma’adinai ba da lasisi ba, masu barnata dukiyar kasa, da kuma rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma har da da masu fashi da makami.
Sannan kuma ya bayyana cewa hukumar tsaron a karkashin sa sun sasanta rikice-rikicen makiyaya da manoma har fiye da 50 a fadin jihar.
Ya ce NSCDC ta bayar da horo na musamman ga jami’an ta su 40 domin kwarewa da gogewa wajen sasanta rigingimu da shiga tsakanin bangarori biyu masu tankiya, tun kafin rikicin ya kai ga kisa ko zubar da jini.
Sannan kuma bangaren masu sa-ido a dazuka da gonaki kuma na hukumar sun tabbatar da cewa manoma sun koma gonakin su, sun ci gaba da noma.
“Hukumar tsaron mu ta kuma tura zaratan jami’an ta a makarantu daban-daban na ckin jihar nan, domin magance hare-hare da hana yin garkuwa da dalibai.” Inji Edem.