Jakadan Najeriya a kasar Mexico, Adejare Bello, ya yi barazanar maka PREMIUM TIMES kotu, saboda haushin ta buga yadda ya zabga wa wani dan jarida mari.
PREMIUM TIMES dai ta buga labari a ranar Juma’a cewa Adejare Bello ya faffalla wa Adeniyi Akinromade, dan jarida mai aiki a Gidan Radiyon Jihar Osun mari, a daidai inda dan jaridar ya tsaya ya na bada hannu, wani wurin da motoci su ka cushe babu wurin wucewa gaba, babu hanyar komawa baya.
Dan jaridar ya yi tunanin tsayawa domin ya taimaka har hanya ta gyaru, yadda kowace mota za ta rika samun damar wucewa.
Ya na cikin bayar da hannu ne sai ga Jakada Adejare Bello a mota tare da jami’an tsaro.
Saboda jin haushin dan jaridar ya daga masa hannu ya tsayar da motar da ya ke ciki, ya bada hannu ga wani bangaren masu motoci, sai jakadan ya fusata, ya fita daga motar da ake tuka shi, ya rika zabga masa tafi, a gaban jami’an tsaron sa.
Shi dai Jakada Adejare, tsohon Kakakin Majalisar Jihar Osun ne.
“Duk da na shaida masa cewa ni dan jarida ne, na fito ne kawai ina bada hannu ga masu motoci, domin a samu saukin cinkoso, sai kawai ya kashe ni da mari a gaban jami’an tsaron sa, kuma ja jama’a na kallo.”
Haka dan jarida Akinromade ya shaida wa PREMIUM TIMES bayan ya sha mari a wajen jakada Bello.
PREMIUM TIMES ta tuntubi jakadan a ranar da abin ya faru, kuma bai musanta marin da ya zabga wad an jaridar ba.
Amma kuma cewa ya yi ya mari dan jaridar ne saboda ya yi tuki, ya bi ta hannun da doka ba ta ce ya bi da motar sa ba.
Sai dai kuma bayan ya kwashi buhun kunya ganin PREMIUM TIMES ta fallasa cewa ya mari dan jaridar ne a wurin da ya ke bada hannu domin taimaka wa motocin da su ka cunkushe a mahadar titi, sai jakadan ya yi barazanar maka wannan jarida kotu.
Lauyan sa mai suna F.O. Abisoye ya kira wannan jarida inda ya nemi a cire labarin cewa ‘Jakadan Najeriya na Mexico ya faffalla wa dan jarida mari’.
Haka nan kuma a ranar yau Talata, wannan jarida ta sake tuntubar jakadan, inda ya kara nanata barazanar zuwa kotu, tare da cewa:
“Idan ku na so ku yi hira da ni, ku zo gida na mana. Amman i ban gaggaura masa mari ba. Wanin ku ya kira ni ranar Juma’a, ban san lambar ko ta wa ba ce. Zan nuna maku abin da doka ta ce. Ina so ku cire wannan labari, kuma ina so shi wancan dan jarida ya furta da bakin sa cewa ya karya dokar tukin mota kan titi.”
Premium Times ta gano cewa tun bayan da aka buga marin da jakada ya yi wa dan jaridar, sai jakadan ya rika tirsasa masa cewa ya ce bai mare shi ba.
Akalla an yi taro sau biyu tsakanin Juma’a da Litinin. Taro na farko da aka yi Juma’a da yamma, har da Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Osun, Lawal Olayemi da Jakada Bello da kuma dan jaridar da aka faffalla wa marin.
Sun rika tirsasa shi wai ya karyata cewa hannu ya ke bai wa motoci, kuma ya ce ya yi tukin ganganci ne, sannan kuma ya ce ba a mare shi ba. Kuma ya bai wa jakadan hakuri.
An kara yin wani taron ganawar inda har lauyan jakadan ya damka wa dan jaridar takardar gargadin ya janye ko a maka shi kotu.
A halin yanzu dai su na ta takura masa cewa ya karyata an daddalla masa mari cikin sa’o’i 24, ko kuma a maka shi kotu.
Yayin da PREMIUM TIMES ta kira Jakada Bello a ranar Talata, bai karyata ya yi taron ganawa da dan jaridar ba, kuma bai karyata cewa ya yi masa barazana ba.
Jami’an ’yan sanda su kuma maimakon su yi magana a kan marin da aka daddalla wa dan jaridar, sai su ka gayyace shi, tambayoyi.
Cikin wata takardar kira zuwa amsa gayyata, jami’an ’yan sanda sun nemi ya kai kan sa Ofishin ’Yan Sanda na Dugbe, da ke Osogbo.
Ana sa ran isar sa ofishin karfe 1:30 na yammacin Talatar nan.
Wakilin mu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Osun, Yemisi Opalola, amma bai same ta ba, domin wayar ta a kulle.
Kwanan nan aka nada Bello Jakadan Najeriya a kasar Mexico, ya na cikin gungun wadanda Buhari ya nada ba da dadewa ba.
Sai dai kuma kungiyoyi daban-daban na ci gaba da yin tofin Allah-tsine ga Bello.
Cikin kungiyoyin har da Kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ), wadda ta nemi Jakada Bello ya gaggauta bai wa dan jaridar hakuri.