Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje wanda aka fallasa shi a wani bidiyo yana karkacewa yana cusa bandir-bandir din dala a cikin babbarrigar sa ya ce bidiyon buge ce kawai don anyi nr don a bata masa suna amma nan bada dadewa ba zai tona asirin wadanda ke da hannu a shirya wannan abu kowa yasan gaskiya.
Idan ba a manta ba Jaridar Daily Nigerian a shekarar 2018 ta wallafa wani bidiyo dake nuna gwamna Ganduje karara yana lale bandir din daloli yana cusawa a aljihun kaftanin sa daga wane dan kwangila wanda ake zargin na goro ne.
A ranar Juma’a, a wata hira ta musamman da gwamna Ganduje yayi da BBC Hausa a cikin shirin ‘Afada Acika’ Ganduje yace wannan bidiyo ta karya ce bidiyon na buge ne aka kirkira kuma wadanda suka fitar da bidiyon zasu sha kunya nan gaba kadan.
“Bidiyon na buge ne, muna shirin tabbatar da hakan, bana so in fada abinda muke yi, amma ina tabbatar maka cewa wadanda ke da hannu wajen fitar da bidiyon za su ji kunya, inji Ganduje.
A halin yanzu Ganduje yana kotu yana kalubalantar mawallafin jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar akan bidiyon da ake zargin an dauka a shekarar 2017, kafin fitar dashi a 2018.
Discussion about this post