Buhari ya yi alluran Rigakafin Korona

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi allurar rigakafin Korona a fadar shugaban kasa.

Likitan shugaba Buhari Suhayb Rafindadi ya tsira wa Buhari allurar da misalin karfe 11 da minti 56 na Asabar.

Bayan an yi masa sai aka bashi katin shaidar yi masa allurar.

Haka kuma shima mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo likitan sa ne yayi masa allurar rigakafin.

Bayan haka Buhari ya hori ‘Yan Najeriya su amince ayi musu rigakafin, yana mai cewa sannu a a hankali za a yi wa sauran’ yan Najeriya rigakafin.

Baya ga kwalaben maganin rigakafin Korona miliyan 4 da ake shigo da su, Najeriya na sauraren wasu kwalaben maganin rigakafin Korona nan da watan Mayu.

Share.

game da Author