Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya cewa su tabbatar da sun samar da tsaro a kasar nan kafin faduwar ruwan damina.
Buhari ya yi wannan gargadin a gare su, ranar Juma’a, a Fadar Shugaban Kasa, lokacin da ya ke daura wa kowannen su maballan zama Manyan Hafsoshi.
An daura wa sabon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Lucky Irabor maballin zama cikakken Janar.
Shi kuma Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Ibrahim Attahiru, an daura masa maballin tabbatar da shi Laftanar Janar. Kamar yadda Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Auwal Gambo ya zama ‘Vice Admiral’, shi kuma Babban Hafsan Sojojin Sama Isisaka Amao ya zama Air Marshal.
An kara masu masu girma wata daya bayan Shugaba Buhari ya nada su tare da mika sunayen su a matsayin wadanda su ka canji su Tukur Buratai.
Wannan karin girma kuma ya zo daidai makonni biyu da amincewar da Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya su ka yi da nadin na su.
An ruwaito Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Femi Adesina ya cewa, “Shugaba Buhari ya umarce su da lallai su tabbatar da samar da tsaro kafin faduwar ruwan dama,yadda manoma za su samu damar fita gonakin su a lokacin ruwan sama.”
“A lokacin da mu ka yi Taron Matsalar Tsaro na tsawon sa’o’i uku ni da ku, a matsayi na na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, na hore ku da tabbatar da tsaro ta hanyar shiga gaba da kan ku a kakkabe kasar nan daga mabarnata.”
“Ku sani cewa ba ku da wani isasshen lokacin da za ku bata lokaci, domin nan da makonni kadan ruwan damina zai sauka. To sai fa mutane sun samu isasshen tsaro sannan za su iya yin ta-maza su fita zuwa gonakin su domin noma abincin da za a ci.” Inji Buhari.