Masu bugawa fasinjojin jirage katin shaidar gwajin Korona na bogi sun shiga hannu

0

Rundunar ‘Yan Sanda da ke Jihar Lagos, ta bayyana bangado wasu gungun ’yan cuwa-cuwar da ake buga wa fasinjojin jiragen sama katin bogi, na shaidar an yi wa fasinja gwajin korona.

Ana wannan binciken ne a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, kama yadda Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da filin jirgin Lagos, Umar Bature ya shaida wa manema labarai a filin jirgin, a ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES a cikin watan Disamba ta buga labarin da Gwamnatin Jihar Lagos ta bayyana cewa ta na zargin akwai masu buga katin shaidar an yi wa fasinjan jirage gwajin korona na bogi, su na sayar wa fasinjoji.

Wadanda aka kama din sun hada da Archibong Odorenyin mai shekaru 34, wanda kuma shi ne mai DAT Cyber Café, wanda kuma shi ne ke bayar da takardar shaidar yi wa mutane gwajin korona ta bogi.

Sai kuma Abdulmalik Ibrahim, mai shekaru 24, sannan akwai Moses Sunday dan shekara 20 kuma ma’aikaci ne da DAT Cyber Café.

Sai kuma wani mai suna Popoola Adewale, ma’aikaci a Patovilki Airport cleaning services.

Yayin da aka damke wadannan mutane su hudu, akwai kuma cikon wasu mutum biyu da su ka dafe keya su ka gudu. Daya Shehu Imam sunan sa, sai kua dayann mai suna Adeola Darlington na Skyblue Services Ltd.

Sannan kuma su na jan hankalin fasinjojin jirage su na karbar masu kudade, har a kan karbi naira 50,000 ga mutum daya.

“A ranar 18 Ga Fabrairu, Popoola Adewale ya karade filin jirgin saman Lagos, ya na neman wanda zai sayar wa satifiket din gwajin korona na bogi.

“Ya je ya tunkari wani mai suna Micheal Osagbogu, wanda ke kan layin shirin shiga jirgin sama mai tafiya London.

“Daga nan su ka kebe da shi cikin wani bandaki, inda su ka karbar masa naira 50,000.

“Daga nan sai su ka damka shi ga wani mai suna Shehu Imam, shi kuma ya dauke shi zuwa wurin Archibong Idorenyin, a shagon intanet mai Lamba 4, Oriyomi Street, Ikeja.’’

Kwamishinan y ace wadanda ake zargin sun amsa laifin su, kuma za a gurfanar da su.

Sannan kuma wadanda su ka tsere su ma ana kokarin cafko su.

Share.

game da Author