Ganin yadda dimbin ’yan Najeriya su ke ci gaba da nuna rashin amincewa da kashe naira bilyan 600 da Gwamnatin Buhari ta ce za ta yi domin a yi gyaran matatar mai ta Fatakwal, Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya fito ya fadi dalilin da ya sa ake so a kashe wadannan makudan kudaden domin a yi gyaran, maimakon a sake kinkimo wani sabon aikin gina wata sabuwa.
NNPC ya ce a yanzu Najeriya ba ta da karfin da za ta iya kashe makudan kudaden da za ta sake gina wata matatar man fetur sabuwa dal a kasar nan.
Mele Kyari ya yi wannan bayanai ne a ranar Litinin a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, wadanda su ka ritsa shi da tambayoyin neman dalilin da za a kashe har naira biliyan 600 domin a gyara matata daya tal ta Fatakwal a wadannan kudade.
Kyari ya ce idan za a sake gina wata sabuwar matatar mai daya a kasar nan, sai an kashe dala biliyan 10. Amma ita matatar Fatakwal, za a iya gyara ta da dala biliyan 1.5, kwatankwacin naira biliyan 600.
Sannan kuma ya kara da cewa, idan Najeriya ta ce za ta gna wata matatar mai a yanzu, to za a ci gaba da shigo da tataccen fetur daga kasashen waje har nan da wasu shekaru hudu masu zuwa.
“Akwai wahala sosai wajen sake gina wata sabuwar matatar mai. Domin ko bincikawa mutum zai yi a Google, zai ga cewa sake gina matatar mai kamar ta Fatakwal zai ci dal biliyan7 zuwa biliyan 12.”
Ya kara da cewa abin da ya sa jama’a ke ganin kudin gyaran matatar mai din kamar sun yi yawa sosai a yanzu, saboda dalewar da matatun suka yi ne ba tare da ana yawan yi masu garambawul da sauran gyare-gyaren kulawa da su ne.
Rijiya Gaba Dubu, Kowa Ya Ki ‘Ya Ba Allah’:
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, da kuma hamshakin atttijir kuma masanin tattalin arziki, wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC, na daga cikin wadanda ba su yarda a narka har naira biliyan 600 wajen gyara matatar mai ta Fatakwal ba.
PREMIUM TIMES ta buga rahoton na musamman kan yadda gwamnatin Buhari ta rika narka makudan bilyoyin nairori wajen gyaran matatun mai, amma a cikin watanni 13 ko danyen mai cikin cokali ba su tace ba.