Najeriya ta ƴan Najeriya ce, idan ka kori Fulani da ƴan Arewa a jihar ka, na ka da suke jihohin mu fa – Gargaɗin gwamnan Bauchi Bala ga gwamnoni

0

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed yayi kira da yin gargaɗi ga sauran gwamnoni da su rika sara suna duban bakin gatari domin tura fa yana neman ya kai bango game da irin muzguna wa ƴan Arewa da ake yi a wasu jihohin Kasar nan.

Bala ya feɗe biri daga kai har wutsiya inda ya yi kira ga shugabanni su rika iya wa bakunan su, suna yi musu linzami.

” Najeriya kasa ce ta duk ɗan Najeriya, Fulani makiyayi yana da ƴanci da damar ya yi kiwo a duk faɗin kasar nan kuma ya zauna da mutane ba tare da an muzguna masa ba.

” A baya Fulani makiyayi na rike makami idan zai fantsama daji kiwo saboda namun dajin da za su yi far masa, shi kuma ya kare kan sa da dabbobin sa. Zamani ya kawo mu yanzu ba namun daji ba ne kawai makiyayi ke kokarin kare kan su da dabbobin su daga har da barayin shanu. Sai kaga makiyayi an far masa da bindigogi a daji an kashe shi sannan an yi awon gaba da dabbobin sa.

” Wannan shine dalilin da ya sa dole shima Fulani makiyayi ya siya bindiga domin irin wadannan mutane. Ya kare kan sa sannan ya kare dukiyar sa.

” Maganan wai Fulani makiyaya su fice daga dazukan wasu jihohi bai ma taso ba. Dazuka dai na gwamnati ne sannan shi makiyayi dan kasa ne. Ba zai yiwu ka hana shi rayuwa ba sannan kai ba ka yi mishi tanadin inda zai koma ba.

” Muma fa a jihohin mu akwai mutanen jihohin da ake korar mana mutane. Anan jihohin bamu taba cewa don an hana mutanen mu wani abu a can ba su ma na nan dole su tashi su koma garuruwan su.

” Gaskiya ɗaya ce kuma ita ce gwamnan Benuwai Emmanuel Ortom shine ya fara ballo wannan matsala da aka shiga yanzu. Sannan kuma ko a jihohin mu akwai ƴan kabilar sa Tivi da Yarabawa a ko ina tare da mu, ba mu ce musu su koma garuruwansu ba.

Gwamna Bala ya karisa jawabin sa da jinjina wa shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, gwamnan Filato, Simon Lalong wanda ya yaba masa kan yadda yake jagoran kungiyar gwamnonin.

Share.

game da Author