Korona ta yi ajalin mutum 68, mutum 5,916 suka kamu cikin kwanaki shida a Najeriya

0

Tunda aka shiga shekarar 2021 Korona ta tsananta a Najeriya fiye da shekarar baya a lokacin da cutar ta bullo a duniya.

Haka kuma mutuwa daga cutar ya karu matuka inda a jere a kwanakin nan sai an samu wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.

Sakamakon gwajin cutar da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na wannan mako ya nuna cewa mutum 5,916 suka kamu da cutar sannan mutum 68 suka mutu a sanadiyyar cutar daga ranar litinin zuwa Asabar, 13 ga Faburairu.

An yi wa mutum 1,398,630 gwajin cutar a kasar nan. Daga ciki mutum 144,521 sun kamu.

Zuwa yanzu mutum 23,921 killace a wurare da aka kebe ana kula da wadanda suka kamu sannan kuma an sallami mutum 120,399. Mutum 1,747 sun mutu.

Jihar Legas, Abuja, Filato, Kaduna, Oyo, Rivers ne suka fi yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.

Hada maganin Korona a Najeriya

Karmar yadda kassshen da suka ci gaba suke rige-rigen haɗa maganin Korona domin mutanen kasashen su, ita ma Najeriya ta ce ta ware wasu kuɗaɗe har naira bilyan 10 domin fara yin gwaje-gwajen fasa kwanya domin ita ma ta haɗa nata domin ƴan Najeriya.

Wani likita da yayi fice a kasar nan ya bayyana cewa wannan magana na Najeriya ta haɗa nata maganin Korona tatsuniya ce kawai domin ko dakin zama ayi tunanin yadda za a hada maganin ma bamu da shi a kasar nan.

Ya ce ware bilyan har 10 don haka sai dai don ko kila a gyara wa wasu miya ta yi ja kawai domin kuwa akwai jan aiki a gaba.

Har yanzu Najeriya na jiran maganin ne daga kasashen waje, wanda tuni ana sa ran za a karbi kwalaben ruwan maganin sama da miliyan daya kafinnkarshen Faburairu.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba, domin mafiyan ƴan Najeriya musamman talakawa su sha alwashin ba za su yarda ayi musu wannan allura ba domin basu amince da ita ba.

Mafi yawan ƴan Najeriya na ci gaba da gudanar da al’amurorin su ba ta re da suna kiyaye dokokin kare kai daga Kamuwa da Korona ba duk da ko gwamnati na gargaɗi akai akai.

Share.

game da Author