An rasa rayukan mutane da yawa a arangamar da ta faru tsakanin Hausawa da Yarabawa, a kasuwar Shasha, da aka fi sani da Sasa, Ibadan, Jihar Oyo.
Rikicin dai ya samo asali ne daga wata gardama tsakanin wasu mata biyu, daga nan fada ya kaure tsakanin wani Bayarabe da Bahaushe, har Bahaushen ya luma wa Bayarabe wuka, ya mutu.
Wanda aka burma wa wuka ya mutu a asibiti, ranar Juma’a, bayan caka masa wukar a ranar Alhamis.
Mutuwar sa ta harzuka Yarabawa, wadanda su kuma su ka yi dandazon daukar fansar kisan da Hausawa su ka yi wa dan uwan su.
Cikin kankanen lokaci sai tarzoma ta goce tun daga cikin kasuwar Shasha, har wajen kasuwa a cikin unguwar Sasa din.
Bangarorin biyu na Yarabawa da Hausawa sun rika kai wa juna hari, da sara, da kisa. Kamar yadda ganau ya shaida wa Premium Times.
“Akalla na ga gawarwakin mutum shida da su ka hada da Huasawa da Yarabawa. An rika banka wa shaguna da kantina na cikin kasuwa.
“Ganin haka kasuwa ta fashe kowa ya tsere kada rikici ya ritsa da shi.” Haka wani mai suna Khalid mazaunin Akinyele ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Wani da rikicin ya faru a gaban sa, amma ba ya so a ambaci sunan sa, ya bayyana wa wakilin mu cewa wannan rikici bai bar kowa ba, domin ya shafi kowa.
“An koma gidaje masu yawa, kuma an kona shagunan cikin kasuwa da dama, kuma an lalata dukiyoyin ‘yan kasuwa. Jama’a da dama sun gudu sun bar gidajen su. Wasu kuma an kona wan a su gidajen wuta.”
‘Na Ga Gawarwakin Hausawa Birjik’
Washegari ranar Asabar kuma matasan Yarabawa ‘yan iska su ka tare hanyoyi, su na binciken motoci.
Duk inda aka ga Bahaushe a cikin mota, sai a fito da shi a rika dukan sa. Wasu kuma a wurin aka rika kashe su.
“In dai kai Bahaushe ne, to kawai za a fizgo ka daga cikin mota a kashe ka kawai. Wai su sun yi haka ne domin ramuwar kisan wani Bayaraben da aka ce wani Bahaushe ya yi a cikin kasuwar Shasha.”
Haka wani wanda ya shaida wa wakilin mu ya bayyana cewa da idon sa ya ga gawarwakin Hausawa birjik a unguwar Moyiwa a ranar Asabar.
Sai dai kuma daga baya an tura sojoji su ka fatattaki masu kisan Hausawa.
Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya shaida cewa komai ya lafa, kuma an gargadi cewa ba za a bari wasu batagari su haddasa fitina ba.
Yayin da gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma ke kiran a zauna lafiya da juna, haka wasu sanarakunan yankin da kuma ‘yan Najeriya da dama.
Tuni dai aka kakaba dokar hana fita a yankunan da rikicin ya kaure.