An bayyana tsadar kayan abinci a cikin watan Janairu da ya gabata, ya yi tashin gwauron zabin da tsawon shekaru 11 bai taba yi ba.
Rabon da farashin kayan abinci ya yi tsadar irin wadda ya yi a cikin watan Janairu, 2021, tun cikin 2008.
Jadawalin wannan kididdigar ya fito ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da kuncin rayuwa sanadiyyar kashe-kashe, garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ke ci gabacda yi, wanda hakan ya dakile kokarin gwamnatin tarayya na farfado da albarkatun noma a karkara.
A cikin wannan halli kuma a daya bangare, gwamnatin tarayya na ci gaba da raba wa matan karkara marasa galihu naira 20,000 kowace, domin samun kama kananan sana’o’in rage radadin talauci.
Malejin tsadar rayuwa ya cilla sama zuwa kashi 20.57 bisa 100 a cikin watan Janairu, 2021, kamar yadda Hukumar Kididdigar Alkaluman Fatara, Talauci da Tsadar Rayuwa ta bayyana.
Ta ce rabon da a samu irin wannan gwauron tashin tsadar kayan abinci a kasar nan tun cikin 2008, tsawon shekaru 11 kenan a jere.
Masu sharhin tattalin arzikin kasa na danganta wannan tsadar kayan abinci da bullar annobar korona, ci gaba da shan duka da naira ke yi a kasuwa a hannun dala da wasu kudaden kasashen waje masu kaurin damtse, wanda aka ce hakan ya haifar da tsadar kayan abincin da ake shigowa da su daga waje.
Wasu dalilan sun hada da yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke wa manoma da takaita zirga-zirgar safarar kayan abinci zuwa kasuwannin wasu kauyuka, saboda fargabar masu garkuwa da mutane.
Hukumar NBS ta ce jihohin da su ka fi jin jiki wajen karin farashin kayan abinci sun hada da Kogi tashin farashin ya kai kashi 26.64, Oyo kashi 23.69 da Jihar Ribas mai kashi 23.49.
Masana da dama wadanda PREMIUM TIMES ta zanta da su, sun bayyana dalilan faruwar haka daban-daban, ciki har da dalilin tashin farashin kudin zirga-zirgar mtocin hayar fasinja da na daukar kaya, wadanda su ka kara farashin jigila saboda karin kudin man fetur da aka rika fama da shi a kasar nan.
Discussion about this post