Jakadan Najeriya a kasar Jamus, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa wani bankin Jamus mai suna KfW da wasu cibiyoyin bada lamuni na Turai sun bayyana sha’awar su ta zuba jari domin aiwatar da aikin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ta cikin Jmahuriyar Nijar.
Titin dai za a gina shi tsawon kilomita 283 ne, kamar yadda ya bayyana a ranar Talata.
Haka Tuggar ya bada albishir a lokacin da ya je Mazabar sa ta Udobo da ke cikin Karamar Hukumar Gamawa jihar Bauchi, domin sabunta rajistar jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa ba kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke rade-radi ba, a yanzu dai ta tabbata Najeriya ta samu cibiyoyin hada-hadar kudaden da za su zuba kudade domin a gina titin Kano zuwa Maradi ta cikin Jamhuriyar Nijar.
Titin a cewar sa, idan aka kammala shi, zai kasance daya daga cikin muhimman ayyukan raya kasa da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gudanar a kasar nan.
“Wannan gagarimin titin jirgin kasa zai bi ta garuruwan Kazaure, Daura, Mashi, Katsina da Jibiya.
“Kuma zai kara bunkasa kasuwanci da cinikayya a wannan yanki sosai.”
Tuggar ya ci gaba da zayyana irin ci gaban da mulkin Buhari ya samar a kasar nan, musamman a bangaren farfado da wasu manyan titinan jiragen kasa a kasar nan da sauran su.
Jama’a da dama na mamakin yadda za a kaddamar da aiki titin jirgin kasa a Kano, alhali wanda aka kaddamar shekaru uku da suka gabata, daga Ibadan zauwa Kano ba a ma fara ba.