Jonathan ya ce ya nan a PDP, gafalallu ke zawarcin sa a APC – Saraki

0

Shugabannin Jam’iyyar PDP sun kai wa Jonathan ziyarar gaggawa, a daidai lokacin da ake ta watsa ji-ta-ji-ta cewa APC na zarawcin tsohon shugaban kasar domin ya tsaya mata takara a zaben 2023.

Shugaban Kwamitin Sasanta Sabani da Rikicin Mambobin PDP, Sanata Bukola Saraki ne ya shugabanci tawagar da ta kai ziyarar a gidan Jonathan na Abuja.

Daga wadanda su ka kai ziyarar akwai Anyim Pius Anyim, Ibrahim Shema, Liyel Imoke da Ibrahim Dankwambo. A wurin akwai Mulikat Adeola-Akande.

Kwamitin dai ya isa gidan Jonathan a ranar Talata da karfe 1;30n na rana.

Baya ga zawarcin da ake yi wa Jonathan ya koma APC, maganganun da ake yadawa na nuni da cewa za a bashi takarar shugabanci a zaben 2023.

Hakan na faruwa ne a lokacin da wasu gaggan PDP su ka canja jam’iyya zuwa APC.

Sannan kuma ana rade-radin baiwa Sanata Danjuma Goje shugabancin jam’iyyar APC. Goje dai tsohon Sanata ne da a yanzu ba ya kan mukamin sanata.

Saraki ya shaida wa manema labarai bayan ziyarar da su ka kai wa Jonathan cewa Jonathan na nan a jam’iyyar PDP, ba zai koma APC ba.

Ya kara da cewa sun kai masa ziyara ne domin sanar da shi irin kokarin da kwamitin su ya yi wajen sanata rashin jituwa da rikicen jam’iyyar da ya faru bayan zaben 2019.

“Ya tabbatar mana cewa shi dai ya na cikin PDP, kuma babu wata APC da zai iya komawa. Sannan ya kara da cewa zai kara bada himma wajen ganin PDP ta kara karfi sosai fiye da karfin ta na yanzu.” Inji Saraki.

“Saboda haka masu neman Jonathan ya koma APC mugaffalu ne, su hakura su daina kawai. Mun same shi, ya tabbatar mana ci gaba da ba mu goyon baya, kuma ya bayyana mana irin goyon bayan da tsoffin shugabbanin kasa irin sa zai rika ba kwamitinmu domin dinke duk wata baraka a cikin jama’iyya da sauran wadda mu ke kokarin dinkewa a yanzu.”

Share.

game da Author