Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 676 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini sannan kuma mutum 21 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –227, Rivers-73, Niger-69, Filato-56, FCT-50, Kano-44, Oyo-43, Ogun-27, Gombe-18, Ondo-15, Enugu-10, Osun-10, Cross River-8, Edo-8, Nasarawa-7, Bauchi-4, Kaduna-3, Ekiti-2 da Zamfara-2.
Yanzu mutum 131,918 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 106,275 sun warke, 1,607 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,036 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Lahadi, mutum 685 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Nasarawa Kano, Akwa-ibom da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –49,501, FCT–16,913, Filato –7,950, Kaduna–7,664, Oyo–5,460, Rivers–5,349, Edo–3,802, Ogun–3,408, Kano–3,036, Delta–2,323, Ondo–2,315, Katsina–1,864, Enugu–1,748, Kwara–1,936, Gombe–1,624, Nasarawa–1,817, Ebonyi–1,423, Osun–1,547, Abia–1,220, Bauchi–1,146, Borno-957, Imo–1,116, Sokoto – 748, Benue- 848, Akwa Ibom–878, Bayelsa 669, Niger–757, Adamawa–631, Anambra–893, Ekiti–579, Jigawa 460, Taraba 412, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–203, Zamfara 205, Kogi–5.
Shugaban fannin dakile yaduwar cututtuka da yin allurar rigakafi na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Bassey Okposen ta bayyana yadda za a yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona a kasar nan.
Bassey ta ce Najeriya za ta karbi kwalaben maganin rigakafin cutar guda 100,000 kyauta. Da wadanna ne za ayi amfani mutane rigakafin kyauta a kasar nan.
Za a saka jami’an tsaro, jami’an gwamnati, jami’an lafiya da wasu masu sa Ido daga kasashen waje a duk wuraren da za a bude domin yin allurar rigakafin a kasar nan.
Bassey ta ce za a yi amfani da maganin ne bayanan hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa.
“Zai dauki hukumar NAFDAC tsawon kwanaki 7 ta tabbatar da ingancin maganin sannan bayan haka a mika maganin ga wani kamfanin wanda zai dauki kwanaki 7 domin ya kara tabbatar da ingancin sa kafin a fara dirka wa mutane.
Bayan haka Bassey ta ce an kasa yin allurar rigakafin zuwa gida hudu. Bayan mutum ya yi allurar farko sai ya yi kwanaki 21 kafin a sake yi masa na biyu da sauran da za su biyo baya.
“Burin Najeriya shine a yi wa kashi 70 na yawan mutanen dake kasar nan rigakafin daga yanzu zuwa 2022.