Kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tsananta tilastwa wa mutane bin dokokin Korona a kasar nan.
Shugaban kungiyar Samson Ayokunle ne ya yi wannan kira a taron wayar da kan fastoci da aka yi a Abuja.
” Tilasta wa mutane su bi dokokin korona zai taimaka wajen rage yaduwar cutar. Saboda haka muke kira ga gwamnati ta tsananta tilasta wa mutane bin dokokin don rage yaduwar cutar.
Ayokunle ya yi kira ga kiristoci da su mara wa gwamnati baya wajen kiyaye dokokin guje wa kamuwa da cutar domin kasar ta samu nasarar dakile yaduwar ta.
Hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA ce ta shirya wannan taro domin wayar da kan fastoci su cigaba da yin kira ga mabiyansu kan kiyaye bin dokokin kare kai.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne hukumar NPHCDA ta shirya irin wannan taro domin wayar da kan malaman adinin musulinci kan amincewa da maganin rigakafin cutar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin kiran da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi na gwamnatin da ta fadada kamfen din wayar da kan mutane game da allurar rigakafin cutar korona da za a shigo da su a watan Faburairu.
Sa’ad ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da rudani da rashin yarda a tsakanin mutane wanda shine yanzu ya karade gari.
“Mutane na yada labaran cewa rigakafin korona gubace kuma anyi ta ne don a kashe mutane Afrika. Amma kada mu manta cewa tun ba yau ake shigo da magunguna daga kasashen waje sannan idan ma ana so a kashe mu din ne ai akwai hanyoyi da dama da za a iya bi ba sai ta rigakafin Korona ba.
Discussion about this post