Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce Najeriya za ta karbi kalaban ruwan maganin rigakafin Korona miliyan 16 ‘AstraZeneca’ a cikin Fabrairu.
Ya ce Najeriya za ta karbi maganin ‘AstraZeneca’ saboda karancin maganin kamfanin Pfizer da ake yi yanzu a fadin duniya.
Shu’aib ya sanar da haka ranar Litini a taron kwamitin PTF da manema labarai a Abuja.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce ta ƙafa asusun COVAX domin samar da maganin rigakafin korona wa kasashe ma su tasowa.
Zuwa yanzu COVAX ta tara kwalaben ruwan maganin Korona sama da biliyan daya kuma zai raba wa kasashe masu tasowa 92.
Asusun ta yi alkawarin samar da maganin rigakafin da zai isa duka kasashe masu akalla kashi 20% na muatanen.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce dalilin da ya sa ake bata lokaci kafin a shigo da maganin rigakafin shine har yanzu masu hada maganin basu yanke shawaran lokacin da za su fara shigowa da maganin ba.
Duk da haka Najeriya za ta karbi kason farko na maganin rigakafin a Fabrairu.
Ehanire ya ce asusun da AU ta kafa AVATT ta yi alkawarin samar da kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona miliyan 41 wa Najeriya.
Ya ce da wannan magani da Najeriya za ta samu zai isa a yi wa akalla kashi 50% na mutanen kasar nan allurar.