JADAWALI: An tsaida ranakun zaben kananan hukumomin Jihar Kaduna

0

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ta tsaida ranar 15 ga watan Mayu, ranar da za a gudanar da zaben Kananan hukumomin jihar 23.

Shugaban hukumar KADSIECOM, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa za a yi zaben ne bayan kammala wa’adin mulki da wadanda ke kan kujerun suka yi da aka zabe su a shekara 2018.

“Kuma daidai da sashi na 25 (1) na Dokar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar mai lamba 2, 2018, za a gudanar da zaben a ranar 15 ga Mayu, 2021, wanda zai kawo karshen shekaru uku da suke kan mulki.

“Sashi na 25 (1) na Dokar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna kamar yadda aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2018, muna sanar da cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar 15 ga Mayu, 2021, tsakanin awanni daga 8 na safe zuwa 4 na yamma,”

Ya ce hukumar ta sanya ranar 26 ga watan Faburairu zuwa 28 ga Maris don gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyya wanda KADSIECOM za ta sa ido don shirya ‘yan takarar su a zaben.

” Jam’iyyu za su karbi fom din takara a ofishin ranar 8 ga Maris.

Sambo ya kara da cewa ranar 21 ga Afrilu, 2021, ita ce ranar karshe na mika fom da jerin sunayen ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka amince da su.

” Har ila yau: “26 zuwa 28 ga Afrilu, 2021, tabbatarwa da kuma tantance fom din da‘ yan takara suka gabatar; 29 ga Afrilu, 2021 za a bayanan ‘yan takarar da aka tantance bayanan su.

” Mayu 2, 2021, ranar karshe da za mika fom din yan takarar da aka tantance da kuma biyan kudade. Ranar 3 ga mayu kuma za a bayyana sunayen dukka yan takarar da za su yi takara a zaben kananan hukumomin.

” 8 ga Mayu 2021 shine ranar karshe da duk wani dan takara da ya ke so ya janye don kan sa, sannan kuma 13 ga Mayu ne ranar da jam’iyyu za su musanya irin wadannan yan takara da suka jan yie don kansu.

” “Ranar 14 ga Mayu, 2021 ita ce ranar ƙarshe na yakin neman zaɓe, yayin da 15 ga Mayu 2021 ita ce ranar zaɓe, ranar 22 ga Mayu kuma ranar da za a gabatar wa wadanda suka yi nasara Satifiket din yin nasara a zabe”

Share.

game da Author