Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kaya na miliyoyin naira a Legas

0

Hukumar kwastam a Legas ta kama wani kwantena dauke da kayan da gwamnati ta hana shigowa da su kasar nan a Apapa.

Shugaban hukumar Malanta Yusuf ya sanar da haka wa manema labarai a garin Legas ranar Alhamis.

Yusuf ya ce hukumar ta kama kwantenan mai lanba SEGU 1793504 dankare da tiles.

Ya ce bayan zurfafa bincike sun gano kwayoyin tramadol har katan 554 da aka boyesu a cikin kwalayen ’tiles’ din.

” Mun kuma kama wani kwantena dauke da maganin sauro wani kuma dauke da kayan gwanjo.

Yusuf ya ce jimlar kudin kayan da suka kama zai kai Naira miliyan 223,225,900.

Bayan haka shugaban hukumar ya ce hukumar ba za ta yi ƙasa-ƙasa ba wajen ganin ta hana shigowa da kayan da gwamnati ta hana shigowa da su.

“Hukumar za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki domin ci gaba da wayar da kan mutane da ‘yan kasuwa sanin illar shigowa da kayan da gwamnati ta hana sannan hukumar za ta dage wajen ganin ta hana aiyukkan ‘yan sumogal a kasar nan.

A makon da ya gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi (NDLEA) ta yi gagarimin kamu na kwayar ‘cocaine’, wato hodal Ibilis har ta zunzurutun kudi naira bilyan 32.

An kama kwayoyin a tashar jiragen ruwa ta Tinka Ila (Tincan Island).

An shigo da dilolin kawayoyin ne cikin Najeriya daga Bazin, wadanda sun kai dauri 40, masu nauyin kilogiram 43.11.

An kiyasta kudin su a arashin kan titi zai kai naira bilyan 32.

Share.

game da Author