Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya bayyana cewa Sanata Smart Adeyemi na Jihar Kogi tantagaryar mahaukaci ne, mai tabin hankalin da ya kamata a ce an gaggauta turawa gidan mahaukata.
Ya kara da cewa Adeyemi na fama da wata cuta, wadda kwakwalwar sa ta kwarkwance, har ya ke furta kalamai wadanda mai cikakkken hankali ba zai iya furtawa ba.
Yayin da Adeyemi ke bayani a zauren Majalisar Dattawa, ya ce Ikpeazu tantirin dan giya ne, kuma gwamnatin sa “gwamnatin ‘yan giya ce, masu sha su yi mankas.”
Adeyemi ya yi wannan kakkausan furucin a lokacin da ake mahawara kan Shirin Kiyaye Lafiyar Dalibai a Makarantu.
“A wasu sassan Najeriya a yau, mu na da masahuran mutane masu kaifin kwakwalwa da basira da zurfin ilmi. Amma jihar kamar Abia, ‘yan giya ne ke mulkin ta, shi kuma gwamnan su ba shi da wani aiki sai shan barasa mai tsada, wato ‘champagne’.
“Al’ummar Abia ba su yi dacen gwamna ba. Al’ummar Abia sun shiga cikin tsomomuwar kuncin rayuwa.” Inji Sanata Adeyemi.
Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labarai na Gwamnan Jihar Abia, mai suna Onyebuchi Ememanka, sai ya fitar da takardar manema labarai, inda ya fassara Sanata Adeyemi da “mutum mai fama da ciwon hauka.”
Ya yi kiran jama’a su yi watsi da shirmen maganganun Adeyemi, wanda ya ce kwakwalwar sa ta tabu, bai fahimci batun ake tattaunawa a majalisa a lokacin da ya yi furucin na sa ba.
“Ku rabu da kwarkwantacce kawai. Kan sa da motsi shi ya sa bai ma san halin da ya ke ciki ba. Ya kamata ya san cewa Jihar Abia ta fi jihar Kogi komai na ci gaba. Kwanan nan fa Hukumar Kididdigar Alkaluman bayanai (NBS) lissafa Abia ta uku a jerin jihohin da masu zuba jari daga waje su ka sa wa albarkar jari. Legas da Abuja ne kadai a gaban Abia.
Daga nan sanarwar daga Gidan Gwamnatin Abia ta ci gaba da yi wa Adeyemi da Jihar Kogi inda ya fito kaca-kaca da gori.