A ranar 22/2/2021 aka tashi da gagarumin yajin aikin masu sana’ar babarun Adaidaita Sahu, wanda ya haifar da matukar koma baya ga fannoni da dama na rayuwa a fadin jihar Kano, domin wannan matsala ta shafi kowa tun daga kan kananun ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa da wasu daga cikin malaman manyan makarantu da kanana, tare da daliban su, duk wannan ya faru ne sakamakon wannan yajin aikin da masu baburan Adaidaita Sahu ke yi.
Bangaren masu Baburan Adaidaita Sahu, sun yi korafin cewa suna fuskantar rashin adalci daga bangaren gwamnati kan yadda ake yi musu tatsar ‘ya’yan kadanya wajen karbar haraji a lokuta daban-daban, wanda hakan shi ya janyo suka yanke shawarar tsunduma wannan yajin aikin, don janyo hankalin gwamnatin domin dakatar da matsin lambar da ake yi musu kan karbar harajin.
Baya-bayan nan dai sun koka kan harajin naira dari da gwamnati ta ce wajibi ne kowanne Mai Babur din Adaidaita Sahu sai ya biya a kullum. In da suka ce hanyar da gwamnatin ta tsara karbar kudin ta yi musu tsauri.
Ita kuma gwamnati a nata bangaren ta bayyana cewa wannan ita ce hanyar da dace wadda babu cutarwa ko wata matsala a cikin ta wajen karbar kudaden harajin daga hannun masu Adaidaita Sahun, don bunkasa kudin shigar da take samu a jihar.
Direbobin Adaidaita Sahun da kungiyoyin su dai sun ce yakamata gwamnati ta saukaka musu hanyoyin yadda za su biya kudin cikin tsari, batare da sai sun je ga hawa nu’urar kwamfiyuta (computer) ba, domin zuwa banki ko yin amfani da na’urar ta kwamfiyuta zai Kara musu wahala ne da bata lokaci tare da karin kashe kudi.
Yayin da ita kuma gwamnati ta ke ikirarin cewa karbar kudi hannu da hannu ya na janyo mata gagarumar asara, domin tana rasa kaso mai yawa daga kudaden da ta ke karbar.
To ko ma dai mene ne, dukan bangarorin guda biyu suna aiki ne don al’umma ta ji dadi. To dai ga shi su al’ummar da a ke yi don su din sun fada cikin wahala da garari mai girma a sakamakon wannan dambarwa, wanda ya janyo musu asara da tashin hankali a cikin kwana daya biyu kacal.
Babban abin takaicin ma shi ne, irin kalaman da ke fitowa daga kowanne bangar, abu ne da ba zai haifar wa al’ummar jihar Kano da da mai ido ba.
Yakamata dai kowanne bangare ya maida wukarsa cikin kube domin kawo karshen wannan al’amari saboda masalahar al’umma, rayuwa ta dawo yadda ta ke ga marasa abubuwan hawa domin su ci gaba da zuwa wuraren ayyukansu cikin sauki da kwanciyar hankali.
A karshe muna kira ga masu ruwa da tsaki da masu fada aji, da su shigo cikin wannan al’amari domin samun mafita.
Allah Ya nuna mana daidai Ya ba mu ikon yin aiki da ita.
Muazu Dan Jarida ne dake aiki da Freedom Radio, Kano.
08036433199
muazumj@gmail.com